Wasu makiyaya dake zama a dazukan dake jihar Ebonyi sun bayyana cewa azabar muzguna musu da mutanen dake kewaye da su ke yi ya kai makura da adalilin haka za su tattara shanun su su canja matsuguni.
Makiyayan sun ce baya ga kashe su da da ake yi, haka kawai sai arika bi a na kashe musu shanu wasu kuma a sace.
” A shekarar 2020, mutum 21 ‘yan uwan mu aka kashe babu gaira babu dalili, sannan kuma sai abi a kashe mana shanu. Ya kai ga yanzu muna zaman dardar ne a wannan jiha ta Ebonyi.
Kuma a duk lokacin da mutanen garin suka afka mana mukan je mu gaya wa ‘yan sanda, kuma su zo su dauki hotuna kamar da gaske amma babu abinda suke yi a akai.
Sai dai kuma rundunar ‘yan sanda sun ce ba bu gaskiya cewa wai duk fulanin dake zaune a jihar ne za su yi kaura. Sun ce a kusan duk lokacin da suka yi bincike sukan gano cewa makiyayan ne suka barnata wa manoma a dazukan gonakin su.
” Sannan kuma ina so in sanar muku cewa ba duka makiyayan bane ko kokarin barin jihar, wani mutum daya ne, kuma mun kama wadanda ke ruruta wutan kiyayya a tsakanin mutane a jihar.