ZAMAN DARDAR: Hasalallu sun kashe sojan da ya harbi farar hula hudu a Maidguri

0

Yanzu haka ana zaman dardar a Maiduguri, babban birnin jihar Barno bayan da hasalallun mutane su ka yi wa wani soja kisan rubdugun taron-dangi.

Sun fusata sun kashe sojan wana aka yi zargin ya bude wa wasu fararen hula su hu wuta.

Wadanda su ka san yadda lamarin ya ke, sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa sojan mai suna Mohammed Abdullahi, ya na da lamba 16NA/7/4272, ya bindige farararen hular su hudu a ranar Asabar, daga wata karamar tankiya a tsakanin su, a Kasuwar Hanyar Baga cikin Maiduguri.

Daya daga cikin wadanda aka bindige din nan take ya mutu, sauran ukun kuma su ka samu manyan raunuka. Yanzu haka su na kwance ana jiyyar su.

An hakkake cewa Abdullahi ya bindige mutanen hudu a lokacin da ya ke mankas da barasa.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ganin yadda ya shimfidar da mutum hudu kwance a kasa, nan da nan hasalallun jama’ar da ke kewayen wurin, su ka rufe shi da duka, har su ka kashe shi.

Kafin kashe shi, Abdullahi ya na tare da Bataliya ta 130, amma kuma an tura shi ne a Bataliya ta 212, a kan aikin dakile ta’addanci a karkashin Operation Lafiya Dole.

Wannan abu ya haifar da zaman dardar a yankin unguwar Barka Da Zuwa, inda fararen hula ke tsoron kada sojoji su dirar wa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, da nufin ramuwar-gayyar kisan da aka yi wa dan uwan su.

Tuni dai wasu su ka arce daga yankin, kada abin ya ritsa da su a lokacin da sojoji za u dirar wa unguwar.

Tuni dai gudun kada abin ya kara haifar da mummunan tashin hankali, sojoji daga Dibijin na 7 sun kewaye unguwar, sun yi mata kawanya.

Sannan kuma an hana fararen hula da sojoji gilmawa wajen. Kuma hukumomi sun ce wurin zai ci gaba da kasancewa a tsare tukunna.

Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya, Burgediya Janar Sagir Musa bai amsa kiran PREMIUM TIMES domin jin ta bakin sa ba.

Shi ma kakakin yada labarai na ’yan sandan Jihar Barno, ya ce bai san komai a kan lamarin ba.

An sha samun matsaloli inda sojoji ke bindige farar hula. Irin haka ce ta harzuka ‘yan Najeriya har su ka yi wa ‘yan sandan SARS bore ko tarzoma.

Share.

game da Author