Za a siyar da kwalban ruwan maganin rigakafin Korona kan dala $3 zuwa $10 a Afrika

0

Tarayyar kasashen Afrika AU ta ce maganin rigakafin cutar Korona da ta tanada za ta siyar da kowani kwalba daya akan dala 3 zuwa 10.

AU ta tanadi kwalaban maganin korona miliyan 270. Najeriya da sauran kasashen Afrika za su sayi maganin rigakafin kan wannan farashi.

Bankin (Afreximbank), ne ya fitar da wannan bayani a ranar Laraba.

Duk da cewa AU ta rage farashin kudin maganin rigakafin wasu na hasashen cewa akwai wasu kasashen Afrika da ba za su iya siyan maganin akan wannan farashi ba.

Rahoton da Afreximbank ya fitar ya nuna cewa kasashen Afrika za su iya samun magani bashi ta rika biya a hankali har zuwa shekaru biyar bayan haka.

Mutum miliyan 3.3 suka kamu a Afrika, mutum sama da 80,000 sun mutu a naihyar.

Najeriya

Bisa ga farashin maganin da AU ta fidda, Najeriya za ta kashe sama da dala miliyan 200 idan za ta sayi kwalabai miliyan 42 din da ta riga ta yo oda don ‘yan kasa.

A lissafe dai Najeriya za ta siya kowani kwalban maganin rigakafin akan Naira 3,183.

Maganin rigakafin Pfizer da Kamfanin COVAX za ta shigo da su za su isa a yi wa ma’aikatan lafiyan dake kula da masu fama da cutar ne kawai allura.

Idan aka kawo maganin AstraZeneca guda miliyan 100 za a siyar da kowani kwalba daya akan dala 3.

Idan maganin Pfizer guda miliyan 50 ne aka kawo za a siyar da kowani kwalba akan dala 6.75.

Kasashen dake karkashin tarrayar Turai da kasar Amurka na biyan dala 19 akan kowani kwaban maganin rigakafin AstraZeneca sannan kasar Isra’ila na siyan maganin rigakafin Pfizer akan dala 30 kowani kwalba.

A yanzu haka babban bankin duniya ya hada hannu da AU domin samar da isassun maganin rigakafin cutar a nahiyar Afrika.

PREMIUMTIMES ta buga labarin yadda kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta koka kan karancin maganin rigakafin korona da ake fama da shi a duniya yanzu

Kungiyar ta ce karancin maganin ya kawo rashin daidaituwa a tsakanin kasashen duniya.

Manyan ƙasashen duniya na ci gaba da warwason maganin don ƴan ƙasashen su, hakan ya sa ruwan magani ya zama gwal sai mai kudi da karfin iko zai mallake shi.

Share.

game da Author