Kotun Daukaka Kara da ke jihar Kano ta yanke hukunci kan wasu matasa biyu da ake zargi da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).
Alkalin Kotun da ya saurari karar ya ce rashin lauya mai tsaya wa Yahaya ya ci karo da dokar kare waɗanda aka tsare bisa ko wane laifi kuma dole ne kotu ta tabbatar da samar masa lauya.
Kotun ta ce za a ci gaba da tsare Yahaya Aminu Sharif, har sai an yi gyara a kan kararsa da aka yi a kotun shari’ar Musulunci a baya tukunna.
Alkalin kotun ya bada da umarnin cewa wani alkali na daban ne zai sake sauraron shari’ar Yahaya Sharif a kotun musuluncin ba wanda ya saurari shari’ar a baya ba.
Idan ba a manta ba a watan Satumbar 2020 wanda aka yanke wa hukunci a kotun mususluncin Yahaya Sharif ya daukaka kara bayan Kotun Shari’ar Musulunci ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Daga nan shi kuma Sharif ya musata zargin da aka yi masa na yin kalaman batanci ga manzon Allah, sannan ya daukaka kara.
Kafin gwamnan Kano Abdullah Ganduje ya saka hannu a kai wanda hakan ne zai sa a tabbatar da hukuncin kotun sai ya garzaya kotun Daukaka kara.
Bayan shari’ar Sharif da Kotun ta yanke hukunci akai, kotun ta kori hukuncin kotun Musulunci da ta kama wani matashi mai suna Umar Faruk da laifi irin haka sannan ta yanke masa hukuncin a daure shi na tsawon shekara 10 a kurkuku.
Kotun ta ce ta yanke wannan hukunci na korara wannan kara ne a bayan gano cewa a lokacin da Farouk ya aikata laifin shekarunsa ba su kai 18 koyu ta sallame shi ya kwata-kwata.
Discussion about this post