Za a kammala titin Abuja-Kaduna-Kano cikin 2023 – Daraktan Aikin Titi

0

Daraktan Aikin Manyan Titinan Najeriya da ke Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Kasa, Funso Adebiyi, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta kammala aikin titin Abuja-Kaduna-Kano cikin 2023.

An dai bada kwangilar aikin titin a ranar 20 Ga Disamba, 2017, yayin da aka fara aikin tun a ranar 21 Ga Mayu, 2018, bisa yarjejeniyar cewa za a kammala aikin cikin watnni 36, wato shekaru uku cif.

“Mun gamsu da yadda aikin ke tafiya da kuma nagartar aikin shi kan sa. Kuma mu na aiki mu ga cewa an kara azama wajen jajaircewa kan ayyukan.

“Ai ku na ganin yadda aikin ke tafiya a lokuta daya daga wancan wuri da na sauran wurare da dama. Kuma bangarorin titin na zuwa da na komawa duk ana aiki a kan su. Kun san titin ya na da tsawon kilomita 375 daga Abuja zuwa Kano.

Daga nan sai daraktan ya roki jama’a da a kara hakuri domin gwamnati na bakin kokarin ta, kuma za ta kammala aikin daidai lokacin da ya kamata, wanda ya ce kuma za a yaba, zai yi karko kuma zai dade sosai.

Daga nan kuma ya roki masu motoci su kara hakuri da takurawar da su ke fuskanta a kan titin a kowace rana, musamman yadda ake yawan saki hanya da kauce hanya da kuma cinkoson motoci.

“Mun yi korari zuwa yanzu, domin har an ci akarfin kilomita 100 na aikin. Duk da dai ba a hade shantal a tsaye aka yi aikin ba, kashi-kashi aka yi shi.

“An kammala kashi 40 na aikin daga Kaduna zuwa Zaria, sai kuma kilomita 70 daga Zaria zuwa Kano.

Share.

game da Author