Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya gargadi masu yada labaran karya game da Korona da su shiga taitayin su cewa duk wanda aka samu yana haka zai dandana kudan sa.
Lalong ya fadi haka ne ranar Laraba.
“Ina gargadin masu yada labaran ƙarerayi game da Korona da su daina domin ni kaina na kama wannan cuta kuma na san irin bakar wahalar da na sha kafin na warke daga cutar.
Ya ce duk wanda aka kama zai dandana kudar sa.
Bayan haka gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda mutane suka yi watsi da bin dokokin Korona a jihar.
Ya ce hakan ya zama abin damuwa a gare sa musamman yadda mutane ke kara kamuwa da cutar kuma ana ta samun karuwar wadanda ke mutuwa.
Lalong ya ce ya zama dole a ci gaba da wayar da kan mutane game da cutar da hanyoyin da za su bi don kiyaye ka su.
Maganin rigakafi
Lalong ya kuma gargaddi mutanen jihar da su nisanta kansu daga yada labaran karya game da maganin rigakafin cutar.
Ya ce a yanzu haka masana kimiya da masana kimiyyar magunguna na jihar na kokarin hada maganin rigakafin cutar a jihar wanda hukumomin kula da inganci da sahihanci magani za su tabbatar da ingancin maganin.