Za a fara cajin naira 15,000 ga mai so a canja masa ranar haihuwa a katin dan kasa – Hukumar NIMC

0

Hukumar Samar da Katin Dan Kasa (NIMC) ta bayyana cewa daga yanzu duk wanda ya ke bukatar canja masa ranar haihuwa daga wadda hukumar ta yi masa rajista da su, to tilas sai ya biya harajin naira 15,000 ga gwamnati.

Kodinetan Shiyya na Hukumar NIMC, Fummi Opesanwo ce ta sanar da haka a Lagos a ranar Laraba.

Sannan kuma duk wanda ya rigaya ya yi rajistar katin dan kasa, amma sai katin sa ya fadi, to zai biya naira 5000 ladar wahalar sake masa wani sabo da gwamnati za ta yi.

Hukumar NIMC dai na karkashin Ma’aikatar Sadarwa da Fasahar Zamani a karkashin Minista Isa Pantami.

Shi kuma wanda za a yi wa gyaran adireshin wurin zama, to naira 500 kacal zai biya hukuma.

Opesanwo ya ce duk da kyauta ake yin katin dan kasa ba biya ake yi ba, to amma gyaran adireshi da canjin ranar haihuwa, sai an biya kudi.

“Gyaran ranar haihuwa za a biya naira 15,000, gyaran adireshi kuma naira 5,00 za a biya. Yayin da sabunta katin da ya bace ko ya lalace kuma a a biya naira 5,000. Wannan ne dalilin da ya sa ake karbar kudade hannun jama’a, amma ba kudaden cuwa-cuwa ba ne ake karba.” Inji Opeanwo.

Ta bayyana cewa kai-tsaye ake biyan kudaden a cikin Asusun Bai-daya na Gwamnatin Tarayya, wato ‘Treasury Single Account.’

Tuni dai aka umarci duk wani mai katin kiran waya ya hada lambobin wayar sa da katin dan kasar sa, kafin nan da ranar 9 Fabrairu.

Wannan lamari ya haifar da cincirindon jama’a a wuraren yin katin dan kasa, a daidai lokacin da korona ke kara fantama a kasar nan.

Jama’a sun yi ta zargin cewa jami’an da ke gudanar da aikin yi wa mutum katin dan kasa su na karbar cuwa-cuwar kudi, har Naira 5,000.

Sai dai kuma Opesanwo ta bayyana yadda lamarin kudaden da ake karbar su ke.

Share.

game da Author