YUNKURIN JUYIN MULKI: An yi wa mutum 92 daurin rai-da-rai

0

Wata babbar kotu a Ankara, babban birnin kasar Turkiyya, ta yanke wa mutum 92 daurin rai-da-rai, bisa ikirarin yunkurin juyin mullki da kotun ta ce ta same su da laifin aikatawa.

Daga cikin wadanda aka yanke wa wannan hukunci dai akwai Janar-Janar da dama, da aka kama tun wani yunkurin juyin mulki a cikin 2016.

Tun cikin 2017 aka fara shari’ar, inda aka fara da gurfanar da mutane 132.

Mutum 12 daga cikin wadanda aka yi wa daurin na rai-da-rai dai an hada masu da aiki mai tsanani a gidan kurkuku.

Hukuncin daurin rai-da-rai gami da aiki mai tsanani, shi ne mafi tsanani a dokar kasar Turkiyya.

Wasu mutum 28 kuma daga cikin su, daurin su bai tsanan ta ba, ya kama daga wa’adin shekaru 19.

Caje-caje da tuhumar da aka yi masu ta kama daga yunkurin aikata kisa zuwa shiga mamba na kungiyar masu ta’addanci.

Kamfanin Dillancin Labarai na Anadolu ya bayyana cewa kotu ta sallami mutum tara, sannan kua akwai wasu mutum uku da su ka rage ba a kai ga kammala shari’ar su ba.

Za a ci gaba da shari’ar sauran mutanen uku.

Ita dai gwamnatin Turkiyya ta zargi wani malamin addinin Musulunci dan kasar, mai suna Fethullah Gulen da ke zaune Amurka da yunkurin shirya juyin mulkin ranar 15 Ga Yuli, 2016.

Rashin nasarar da juyin mulkin ce ta haifar da gwamnatin Shugaba Tayyeb Ordogan tashi tsaye ta kama dubban mutane ta garkame.

Sai dai Gulen, wanda tsohon aminin Ordogan ne, ya musanta hannu a yunkurin juyin mulkin, wanda ya janyo asarar rayukan sama da 250.

Share.

game da Author