Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta gano wani gida da ake killace mata masu ciki kuma ake siyar da jarirai a jihar.
Kakakin rundunar’ Yan sandan, Haruna Mohammed ya sanar da haka ranar Laraba a garin Awka.
Kakakin ‘yan sanda Mohammed ya ce sun kama mata har goma dake da hannu a wannan sana’a sannan sun kwato jarirai biyar a wannan gida bayan wasu’ yan mata 3 da ka same su dauke da tsohon ciki suna gab da su haihu a kwashe ‘ya’ yan a biya su kudin su.
Ya kuma ce rundunar ta ceto wasu kananan yara guda uku a kauyen Oba dake karamar hukumar Idemili.
“An gano gidan siyar da jariran ne a kauyen Oba dake Idemili ta Kudu.
“Bincike ya nuna cewa wata mata mai suna Uju Uba ce ke da gidan wanda ke kusa da asibitin koyarwa na jami’ar Nnamdi Azikiwe.
“Rundunar ta kama Edna Nnadi mai shekaru 37, Ujunwa Nweke mai shekaru 25, Izuchukwu Uba mai shekara 24, Chinasa Ibeh mai ahekara 19, Peace Effiong Mai shekara 25, Gift Collins Mai shekara 20, Chimkaso Kingsley Mai shekara 25, Happiness Monday mai shekaru 18, Chioma Okonkwo mai shekara 25 da Uchechukwu Nwankwo, mai shekara 18.
” Mata biyar daga cikinsu na dauke da tsohon ciki.
Mohammed ya ce rundunar za ta kai yara ukun da jarirai biyar din da ta kwace su daga gidan zuwa ma’aikatar kula da al’amuran mata da yara kanana na jihar.
Ya kuma ce rundunar za ta ci gaba da yin farautar gidaje irin haka domin kamo ire-Iren mata haka da ke kasuwancin jarirai a jihar.
Discussion about this post