Masu garkuwa da mutane sun yi gaba da basaraken gargajiya na jihar Adamawa, Ardo Mustapha.
Sun tafi da shi, bayan sun ritsa shi a gida, wajen karfe 12 na tsakar dare, Mayo-Farang, cikin Karamar Hukumar Mayo Belwa.
“ An sace shi bayan isar sa gida ke da wuya ba da dadewa ba, daga Abuja.
“ Sai dai kuma maharan da dogaran da ke tsaron basaraken sun bude wa juna wuta, kafin a yigaba da basaraken.
“ Abin babu dadi ko kadan, kuma abin takaici ne. Kuma har yanzu masu garkuwar ba su tuntubi lambar wayar kowa ba, ballantana har a ji ta bakin su.”
Haka wani makwaucin sa da ke cikin halin kidimewa ya shaida wa wakilin PREMIUM TIMES a safiyar Talata.
Kakakin Yada Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Adamawa, Suleiman Nguroje, ya tabbatar da yin garkuwa da basaraken, kuma ya ce jami’an su na bakin jokarin farautar masu garkuwar, domin su ceto shi.
“ Lokacin da mu ka ji labarin sace basaraken, Kwamishinan ‘Yan Sanda ya tashi zaratan jami’an kar-ta-kwana domin bazama ceto shi.
“A yanzu haka ana biye da su, kuma da an cim masu za a ceto shi da iznin Allah.”
“ Ita harkar tsaro ta kunshin kowa, kuma ta na bukatar goyon baya da hadin kan kowa. Don haka a rika ba mu labarin duk wani mutumin da ba a yarda da shi ba, ko wanda ake zargi.”
Discussion about this post