Shugaban kwamitin Shugaban Kasa na PTF Boss Mustapha ya bayyana cewa ‘yan bautan ƙasa 731 sun kamu da cutar Korona a Najeriya.
Mustapha ya fadi haka a ganawar kwamitin da manema labarai a Abuja ranar Talata.
Ya ce an gano haka ne bayan gwajin cutar da aka yi wa ‘yan bautan ƙasar na rukuni na B su 35,419 a duka sansanonin dake fadin kasar nan.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya gwamnati ta yi wa ‘yan rukunin farko wato A gwajin cutar inda daga ciki aka samu masu bautar kasa 108 sun kamu.
Bayan haka watanni biyu da suka gabata PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda ‘yan bautan ƙasa 138 suka kamu da korona a fadin kasar nan.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,204 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –654, FCT-200, Filato-60, Kaduna-54, Kano-40, Rivers-30, Edo-28, Nasarawa-25, Kebbi-19, Bauchi-18, Oyo-13, Akwa Ibom-12, Bayelsa-11, Ogun-11, Delta-9, Abia-8, Benue-5, Imo-3, Borno-2, Sokoto-1 da Osun-1.
Yanzu mutum 91,351 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 75,699 sun warke, 1,318 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 14,267 ke dauke da cutar a Najeriya.