Yadda za a yi wa mutane rigakafin Korona a Najeriya – Bassey

0

Shugaban fannin dakile yaduwar cututtuka da yin allurar rigakafi na hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko NPHCDA Bassey Okposen ta bayyana yadda za a yi wa mutane allurar rigakafin cutar korona a kasar nan.

Bassey ta yi bayanin haka ne a Shirin ‘Sunrise daily show’ na talbijin din ‘Channels TV’ ranar Asabar.

Ta ce Najeriya za ta karbi kwalaben maganin rigakafin cutar guda 100,000 kyauta. Da wadanna ne za ayi amfani mutane rigakafin kyauta a kasar nan.

Za a saka jami’an tsaro, jami’an gwamnati, jami’an lafiya da wasu masu sa Ido daga kasashen waje a duk wuraren da za a bude domin yin allurar rigakafin a kasar nan.

Bassey ta ce za a yi amfani da maganin ne bayanan hukumar NAFDAC ta tabbatar da ingancin sa.

“Zai dauki hukumar NAFDAC tsawon kwanaki 7 ta tabbatar da ingancin maganin sannan bayan haka a mika maganin ga wani kamfanin wanda zai dauki kwanaki 7 domin ya kara tabbatar da ingancin sa kafin a fara dirka wa mutane.

Bayan haka Bassey ta ce an kasa yin allurar rigakafin zuwa gida hudu. Bayan mutum ya yi allurar farko sai ya yi kwanaki 21 kafin a sake yi masa na biyu da sauran da za su biyo baya.

“Burin Najeriya shine a yi wa kashi 70 na yawan mutanen dake kasar nan rigakafin daga yanzu zuwa 2022.

Share.

game da Author