Dan majalisan dake wakiltar shiyyar Gwadabawa da Illela a majalisar tarayya, Abdullahi Salame ya bayyana yadda yayi batakashi da ‘yan fashi a lokacin da suka afka masa a gidan sa dake Sokoto.
Samame ya bayyana yan fashin sun dira gidansa ne da misalin karfe Uku na dare. Daga nan suka rika batakashi a tsakanin su har Allah ya bashi ikon bindige daya daga cikin su sannan wasu da dama suka arce da rauni a jikin su.
kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto Mauhammad Sadiq ya tabbatar da aukuwar wannan lamari inda yace ‘yan sanda sun kai masa dauki a lokacin da abin ke faruwa.
” Allah ya sa mun fatattake barayin cikin dare. Ya yi kira ga mutane su rika gaggauta sanar da ‘yan sanda irin haka.