Tunda aka shiga sabuwar shekarar 2021 Korona ta tsananta a Najeriya fiye da shekarar baya a lokacin da cutar ta bullo a duniya.
Haka kuma mutuwa daga cutar ya karu matuka inda a jere a kwanakin nan sai an samu wadanda suka rasu a dalilin kamuwa da cutar.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,883 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –1040, FCT-298, Anambra-86, Rivers-54, Taraba-45, Ogun-42, Oyo-40, Akwa Ibom-38, Sokoto-30, Ebonyi-30, Imo-28, Kaduna-28, Osun-27, Kano-21, Benue-19, Edo-17, Gombe-15, Ekiti-9, Delta-8, Jigawa-3, Kwara-2, Bayelsa-2 da Filato-1.
Yanzu mutum 130,557 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 103,712 sun warke, 1,578 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 25,267 ke dauke da cutar a Najeriya.
Ranar Alhamis, mutum 1114 suka kamu a Najeriya, jihohin Filato, Ondo, Kaduna, Oyo da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –48,919, FCT–16,863, Filato –7,892, Kaduna–7,603, Oyo–5,404, Rivers–5,260, Edo–3,779, Ogun–3,356, Kano–2,952, Delta–2,323, Ondo–2,288, Katsina–1,838, Enugu–1,738, Kwara–1,936, Gombe–1,606, Nasarawa–1,764, Ebonyi–1,423, Osun–1,516, Abia–1,220, Bauchi–1,142, Borno-946, Imo–1,116, Sokoto – 748, Benue- 848, Akwa Ibom–845, Bayelsa 669, Niger–688, Adamawa–631, Anambra–893, Ekiti–568, Jigawa 460, Taraba 412, Kebbi 267, Yobe-241, Cross River–195, Zamfara 203, Kogi–5.
Najeriya ta fantsama neman maganin Kotona
Cibiyar Binciken Lakanin Hada Magunguna ta Kasa, NIPRD, ta bayyana cewa ta gano wasu sinadarai da lakanin da idan an harhada za a iya samar da maganin warkar da cutar Korona.
Babban Daraktan Cibiyar Pharmaceutical Research and Development (NIPRD), Obi Adigwe ne ya bayyana haka a Abuja.
“Tun kimanin tsawon shekara daya kenan, mu ka yi amfani da kwarewa da kuma fasahar kimiyyar da muka koya, har muka gano cewa Nipprimmune’ zai iya maganin cutar korona.” Inji Adigwe.
“A wancan lokacin fa mun rika karade gidajen talbijin daban-daban, mu na sanar da abin da muka binciko, tare da rokon masu tallafawa su shigo ciki a yi hadin guiwar sa kudade domin mu karasa abin da ya rage kafin mu kai gacin tabbatar da maganin, har ya wadata yadda za a rika amfani da shi.”