Wata matan aure mai sana’ar siyar da maganinn gargajiya jiko da tsimi da ake kira Agbo, Rofiat Biliameen ta kai kara kotu a Ibadan, ta na so kotu ta raba auren da ke tsakaninta da mijinta Ahmed Biliameen, saboda zalintarta da yake yi.
Rofiat dake zaune a unguwar Ayegun-Olomi ta ce ta gaji da zaman aure a gidan Ahmed saboda ta gano ashe tun farko kwanta-kwanta yayi mata, yayi mata gadan zare ta ko fada ruf.
Tace ta gano Ahmed dai mugu ne kuma azzalumi domin har barazanar kashe ta yake yi yanzu.
Ta kuma gabatar da wasu hujjoji a gaban kotun.
“Mijina ba mutumin kirki bane kuma kowa ya San shi da halin banza a unguwar mu. Saboda tsananin muguntarsa da hassada da ya ke min har kulle-kulle yake yi ya gurgunta ni da sana’ata.
Rofiat ta ce ta a dalilin neman gidan haya muka hadu da Ahmed, ya taya ni neman gida. Sai dai kuma gidan da ya sama min ya ce mai aure ake so a baiwa. Shi ke nan ya yi ta min dadin baki cewa dama yana neman mata mu yi aure kawai mu zauna tare.
” Yanzu ina bin Ahmed bashin Naira 175,000 da ya karba bai biya ni ba har yanzu.
Sai dai bayan ta gama bayanan ta, mijin Rofiat, Ahmed ya karyata duk abin da ta fadi a gaban alkali.
Ya ce Rofiat muguwar mata ce domin ya gano makircin da take shiryawa na ta kwashe duk abinda ya mallaka ta gudu, sai Allah ya tona mata asiri.
Ya ce ya gina wa matarsa shago sannan ya siya fili ya bata Kuma duk da kudin shi ya yi haka.
“Da na gane muguwar mata ce sai na kaurace mata kawai na kuma gwalo idanu na da kyau ya kallonta kawai, shine ta fusata ta kawo kara kotu.
Alkalin kotun Odunade ya dage zaman kotu kan karan sai 11 ga Faburairu 2021.