Yadda cutar ‘Calicivarus’ ta haddasa wa masu kiwon zomaye dibga asara

0

Wata cutar da ke kashe zomaye farat-daya mai suna RHDV ta bulla a jihar Oyo, inda ta haddasa gagarimar asara ga masu kiwon zomaye a jihar.

Wannan cutar dai da aka fi sani da Calicivirus ta fara bayyana ne a China cikin 1984, kuma an hakkake cewa kashe zomaye ta ke yi farat-daya, sau tari da yawa ma ba a ganin wata alamar cuta a jikin zomo kafin ya bingire ya mutu.

Ana matukar bukatar naman zomaye dai wajen gina jiki da kuma kariya ga kandagarkin hana cututtuka shiga jikin mutum.

Sai dai kuma bullar wannan cuta a jihar Oyo ya haifar da matsala ga kiwon zomaye da kuma karancin sa matuka.

Wata mai kiwon zomaye, mai suna Oyelami Josephine, ta ce ta yi asarar zomaye har 350 manya-manya, da kuma kananan sabuwar haihuwa har guda 150, tun daga barkewar cutar cikin watan Yuni.

Josephine ta ce akalla ta yi asara za ta kai ta naira miyan biyar, kudin da ta ce sun gurgunta sana’ar ta sosai.

“Yanzu dai na yi wa garken kiwon zomaye na feshin magani ya fi sau hudu. Kuma duk wani matakin kauce wa sake kamuwa da zomayen da zan fara kiwo a yanzu, duk na dauka.”

Shi kuwa wani mai suna Onalapo Farouq, cewa ya yi wannan cutar zomaye ta shiga ko’ina a gonakin kiwon zomaye da dama.

Farouq wanda ke da Oayimika Farms, Oyo, ya bayyana cewa, “Na yi asarar zomaye 57, kuma duk zomo daya dankarere babba ana sayar da shi naira 23,000. Akwai ‘yan naira 10,000 da na naira 8,000 da na naira 4,000.

“Gaba daya dai na yi asara ta kudin zomaye naira 567,000.

Shi kuwa Mataimakin Shugaban Kungiyar Masu Kiwon Zomaye na Jihar Oyo, Abayomi Okunade, ya ce ya yi asarar kananan zomaye na naira milyan 1.

Ya yi korafi da kuma nuna damuwa cewa masu kiwon zomayen ne da kan su ke ta gaganiyar magance wannan cutar da ke kashe zomaye da kan su, ba tare da sa hannun gwamnati ba.

“Da feshin magani da komai duk mu ke yi da kan mu. Saboda gwamnati ba ta ma san mu na duniya ba. Ba ta san da wasu masu kowon zomaye a jihar Oyo ba. Mu da kan mu ke ta kokarin wayar wa junan mu da kai dangane da wannan cutar da ke ta kamshev mana zomaye.” Inji shi.

Sai dai kuma Daraktan Harkokin Noma da Albarkatun Kasa na Karamar Hukumar Akinyele, Ibekunle Abiodun Ismail, ya bayyana cewa gwamnati na da kudaden da za ta iya agaza wa masu kiwon zomayen.

Ya ce ana yi wa masu kiwo da noma horo, kuma za su nemi ramcen kudi a ba su. Saboda akwai hukumomin da ke bayar da lamunin kudaden kamar bankuna da sauran su.

Ya ce ma’aikatar su aikin ta bayar da horo da kuma wayar masu da kai ta hanyar amfani da gidajen radiyo da sauran su.

“Kuma mu na yin allurar rigakafi a duk shekara ga manya da kananan dabbobi.” Inji shi.

Wani manazarcin cututtukan dabbobi da ke Jami’ar Ibadan, Dakta Gbenga Alaka, ya bayyana cewa wannan cutar zomaye bakuwa ce a Najeriya.

Ya ce sai ma a cikin watan Agusta aka fara gano cutar ta bulla a jikin zomaye.

“Mun yi amanna cewa wannan cutar da ke kashe zomaye farat-daya, ta shigo kasar nan ta hannun masu fita waje su na karambanin sayo zomayen kwalisa masu tsadar tsiya su na shigo mana da su kasar nan.” Inji shi.

Ya bada shawarar a daina shigo da zomaye barkatai, kuma a rika killace zomaye tare da rika yin feshi.

Sannan kuma ya bada shawara cewa masu kiwon zomaye su rika wanke hannu, wanke tufafin su da sauran matakan tsaftar da su ka wajaba.

Share.

game da Author