Wadannan Manyan Hafsoshin Tsaron Kasa dai an sauke a karshe bayan sun kai kusan shekaru su na aikin soja.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya tsige Buratai da sauran Manyan Hafsoshin Tsaro, ya nada sabbi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da takardar sanarwar ajiye aiki da Manyan Hafsoshin Tsaron Kasa su hudu su ka yi.
Wadanda su ka ajiye aikin sun hada da Hafsan Hafsoshin Sojoji, Tukur Buratai, Babban Hafsan Tsaron Kasa, Ganar Abayomi Olonisakin, Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Vice Admiral Ibok Ibas da kuma Air Marshal Sadique Abubakar, Babban Hafsan Sojojin Sama.
Wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Shugaba Buhari, Femi Adesina ya wallafa a shafin sa na Facebook, ta ce Buhari ya yi wa hafsoshin fatan alheri a dukkan al’amurran da su ka sa gaba bayan ritayar da su ka yi.
An maye guradun su da Manjo Janar Leo Irabor, matsayin Babban Hafsan Tsaron Kasa, Manjo Janar I Attahiru, matsayin Babban Hafsan Sojoji wanda ya canji Buratai, Rear Admiral A.Z Gambo, Babban Hafsan sojojin Ruwa, sai kuma Air-Vice Marchal I.O Amao, Babban Hafsan Sojojin Sama.
Buhari ya taya sabbin manyan hafsoshin kasar da ya nada murna, kuma ya yi horo gare su su kasance masu biyayya da aiki tukuru kan ayyukan da aka dora wa kowanen su.
Wadanda aka tsige din dais u ne su ka fi sauran manyann hafsoshin tsaron kasa dadewa a kan aiki tun bayan samun ‘yancin Najeriya.
Sannan kuma dadewar da su ka yi kan aiki har tsawon wattani 66, ya haifar da ka-ce-na-ce da korafe-korafen a tsige su, saboda matsalar tsaron da aka yi tunanin za su iya magancewa, ta ki ci ta ki cinyewa
A ka’ida, duk wanda ya shiga sojan Najeriya a matsayin sa kai, to ba zai wuce shekaru 18 a aikin soja za a yi masa ritaya ba.
Shi kuwa gangariyar soja, a ka’ida ba zai wuce shekaru 60 a duniya ba ya na aikin soja. Ko kuma kada ya shafe shekaru 35 a cikin aikin soja.
Sai dai kuma su Buratai su hudu sun shafe tsakanin shekaru 36 zuwa 40 su na aikin soja, abinda ya saba wa dokar kasa.
An nada su ranar 13 Ga Yuli, 2015, kuma cikin Disamba, 2017 aka sabunta masu karin wa’adi, kamar yadda PREMIUM TIMES ta ruwaito a lokacin.
Sai dai kuma bayan shakaru biyar sun a kan mukamai, sun kasa shawo kan matsalar tsaro, kamar yadda PREMIUM TIMES ta buga a ranar Talata, ranar da aka tsige su.
Olonisakin, Babban Hafsan Tsaron Kasa, ya shafe shekaru 40 ya na aikin soja, kuma shi ne soja mafi girman mukami a Najeriya. An dauke aikin soja tun cikin 1981.
Shi ma Buratai ya shiga aikin soja tun cikin Janairu, 1981, ya yi shekaru 40 cif cikin aikin soja.
Babban Hafsan Sojojin Sama Siddique kuwa tun cikin 1979 ya shiga aikin soja.