Yadda budurwa ta sace jaririyar matan saurayinta da katin ATM ta gudu da su

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo sun bazama farautar wata mata mai suna Temitọpẹ Adeniyi da ta saci jaririya da katin ATM din matar saurayinta.

Wannan abin mamakin da ban haushi ya auku ne a watan Janairu 2021 a unguwan Oke-Bola dake garin Ondo.

A watan Disamba Wasiu Mamukuyomi ya kawo wa matarsa budurwarsa Temitọpẹ ta koya mata dinki, domin ita Tela ce.

Stella Mamukuyomi matar Wasiu ta ce tun da mijinta ya kawo yarinyar ta fara zargin akwai wani alaka na kud da kud tsakanin ta da mijinta.

“Wasiu ya kawo budurwarsa Wanda ban taba sani ba shago na domin ta koyi dinka kaya.

“Sai dai na lura cewa yarinyar na yawan magana da mijina a wayar a lokacin da muke aiki.

Stella ta ce ranar 2 ga Janairu da Temitọpẹ ta zo shago sai ta karbi ‘yar jaririyarta ta yi mata wanka sannan ta nemi izinin goya jaririyar domin ta yi barci.

Bayan dan wani lokaci sai na dauko katin ATM na aiketa wato Temitọpẹ ta ciro min kudi Naira 3,000 a hannun masu POS dake kusa da mu.

“Tun da na aiki Temitọpẹ ban sake saka ta a ido. Ta gudu da ‘Ya ta, kudin da ana aiketa da katin ATM dina.

Stella ta ce ta kira mijinta a waya amma bai amsa ba, kuma da ya dawo, bai ce mata komai akai ba sannan bai nuna wani tashin hankali.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Leo Tee-Ikoro, ya ce a yanzu haka Wasiu na hannun jami’an tsaro sannan yana taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen kamo Temitọpẹ.

“Wasiu ya bayyana wa jami’an tsaro cewa Temitọpẹ budurwarsa ce, ya biya kudin dakin hayan da take zama sannan ya kawo ta wajen matarsa domin ta koyi dinkin.

Tee-Ikoro ya ce Wasiu ya musanta sanin sace jaririyar da budurwarsa ta yi
Sai dai jami’an tsaron na zargin cewa Wasiu karya yake yi yana da masaniyar sace jaririyar da budurwarsa ta yi.

Tee-Ikoro ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin kamo Temitọpẹ.

Share.

game da Author