PREMIUM TIMES HAUSA ta kara binciken da ta gano cewa ’yan Boko Haram masu yawa sun samu damar shiga cikin garin Geidam salum-alum ne ta hanyar ajiye motocin su bayan garin, inda daga nan su ka taka a kasa, su ka darkaki cikin garin.
Sannan kuma wadannan ’yan ta’adda sun shiga cikin kasuwar garin, su ka kama wuri kowa ya lamfale, ya na jiran lokacin da za su fara kai farmaki ya yi.
Da ya ke bayyana mugun shirin da maharan Boko Haram su ka yi, Kakakin Yada Labarai na ‘Yan sanadan Jihar Yobe, Dungus Abdulkadir, ya ce tun wajen karfe 1 na rana aka fara baza ji-ta-ji-ta a cikin kasuwa cewa an ga gilmawar Boko Haram, wanda hakan ya sa kasuwar ta fashe, kowa ya tsere.
Rashin Sani Ya Fi Dare Duhu: Yadda Aka Ci Kasuwar Geidam Tare Da ‘Yan Boko Haram:
“Sai dai kuma bayan kasuwa ta fashe wajen karfe 1 yayin da aka ce an ga gilmawar ‘yan Boko Haram a ciki, daga baya wajen karfe 2:30 na rana kuma sai aka rika karyata ji-ta-ji-tar, inda jama’a su ka rika komawa cikin kasuwa, su ka ci gaba da gudanar da harkokin su. Amma kuma duk da haka dai jami’an tsaro sun ja daga a cikin shirin ko-ta-kwana.
“ Ashe jama’a ba su sani ba cewa Boko Haram sun ajiye motocin su a bayan gari, sun shiga Geidam da kafa ne, kuma da daman su sun samu wurare daban-daban sun yi shirin kai farmaki.
“Ai fa wajen karfe 5:30 na yamma, sai su ka fara kai hare-hare cikin garin, su ka darzaza kai-tsaye gidan Hakimin Geidam, kuma su ka yi awon-gaba da shi.
“Daga nan kuma su ka dumfari gidan tsohon shugaban karamar hukumar Geidam, su ka bamka masa wuta. Sauran ‘yan Boko Haram kuma su ka rika banka wa shaguna wuta, wasu kuma na kwasar kayan abinci da magunguna.” Haka Abdulkarim ya bayyana.
Ya kara da cewa harbi ya samu wata karamar yarinya, wadda aka garzaya da ita asibiti. Kuma a lokacin da ake rubuta labarin ta na kara samun sauki.
“Sun kuma zarce gidan Lawani, amma su ka kasa shiga. Watakila sun yi tunanin ko ba ya ciki a lokacin. Ko kuma sun yi tunakin kawai su kyale shi. Ba mu dai sani ba kam.
“Sun banka wa wata mota kirar Hilux wuta. Akwai mutum biyu accikinn ta lokacin. Motar da ta na hannun mu. Mutanen biyu kuma ana cewa Boko Haram ne. Amma dai ba mu tabbatar ba.
“Jami’an kiwon lafiyar da su ka kama kuma ba su tafi da su ba. Sun dai yi amfani da su wajen kula da Boko Haram din da aka ji wa ciwo. Daga nan kuma su ka kyale su, ba su tafi da su ba. Kun ga kenan ba za a ce an yi garkuwa da sub a. Haka dai sakamakon binciken da jami’an tsaro su ka gudanar ya tabbatar.
Tuni dai Gwamnan Jihar Yobe ya umarci a gaggauta bayar da agajin gaggawa ga masu shagunan da aka kona wa kadarori da sauran wadanda harin yac shafa.