An dakatar da wasu daraktocin Hukumar Sa-ido Kan Safarar Tantagaryar Kudade (NFIU), saboda sun assasa binciken Atiku Abubakar da Bola Tinubu.
Wadansu sahihan takardun bayanan da su ka fado a hannun PREMIUM TIMES su ka tabbatar da haka.
Wadanda aka dakatar din su ne Darakta Mohammed Mustapha, wanda shi ne daraktan Sa-ido da Binciken Kwakwaf, sai kuma Daraktan Nazari da Tantancewa, Fehintola Salisu.
An dakatar da su tun cikin watan Agusta, 2020,saboda sun rubuta takardun bada umarni ga hukumomin cikin gida da na kasashen waje cewa su bincike gaggan ‘yan siyasar na Nejeriya su biyu.
Daraktan Hukumar NFIU, Modibbo Tukur, wanda aka nada cikin watan Janairu 2020, shi ne ya dakatar da su a ranar 13 Ga Janairu, 2021, a bisa dalilin sun aika da takardun neman a binciki Atiku da Tinubu, ba tare da iznin sa ko shawara da shi ba.
Su biyun dai duk su na da muradin tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben 2023.
Su biyun da aka dakatar dai ana ganin su kadai ne jami’an da su ka rage a hukumar, wadanda ake ganin masu sauran karsashin dadewa a hukumar.
Tukur ya ce an dakatar da daraktocin biyu ne domin a haka irin daukar gaban-gabatar ayyukan da ba daidai ba da su ka dade su biyun su na aikatawa.
Ya ce abin da su ke aikatawar zai iya zubar da martabar NFIU.
An dai dauki hukuncin dakatarwar a kan su ne, bayan da aka aika wa Hukumar ICPC takardar korafin abin da aka yi zargin sun aika, wanda hukumar ke ganin zagon-kasa ne ga aikin ta.
Wani ofishin lauyoyi mai suna C. Chris Ekemezie & Associate ya rubuta takardar korafi kan Tukur, a cikin 2019 ga ICPC.
Mai korafin ya zargi su Tukur da kokarin bin-diddigi da ingiza binciken wasu manyan ‘yan siyasar jihar da ya fito.
Atiku Abubakar dai da Tukur duk ‘yan Jihar Adamawa ne.
Daidai gabatowar zaben 2019, Ministan Harkokin Yada Labarai, Lai Mohammed ya ce ana zargin Atiku da hannu wajen durkushewar Bank PHB.
Ba a sani ba ko wannan batun ne Mustapha ya nemi kokarin sake tayarwa.
Sai dai kuma Tukur ya ce batun kokarin tayar da binciken Atiku ba shi da wata alaka dakatar da su Mustapha.
“Mustapha ya rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya da kuma Shugaban Hukumar EFCC wasiku, abin da ya kauce wa tsarin aikin da aka dora shi ya yi.
Kuma kafin sannan, na sha rubuta wa ma’aikata wasikun sanarwa da gargadi da kuma furtawa baki dabaki cewa ma’aikata su daina rubuta wa shugabannin hukumomin binciken laifuka kudade wasiku kai-tsaye.”
Tukur ya rubuta wa Shugaban ICPC wasika cewa bai san Mustapha ya rubuta wasika ga Sufeto Janar da Shugaban EFCC ba, har sai bayan da Fadar Shugaban Kasa ta sanar da wani kokari da Atiku ya yi na ganin shugaba Buhari.
“Haka kuma Mustapha ya rubuta wa Amurka wasika a kan Tinubu, dangane da matsalar sa da hukumar CCB.
Daya matar da aka dakatar tare da Msutapha, ta na da hannu a cikin rubuta takardar binkikar Atiku, ba tare da dalilin hakan ya taso ba.
Tukur ya kara da cewa dalilin dakatar da Mustapha, daboda EFCC da SSS na binciken sa kan laifin fallasa batun tsohon Babban Jojin Najeriya, Onnoghen ga bainar jama’a.
Sannan kuma ya bude asusun ajiyar banki da sunan FIU ba tare da izni ba.
“Ni ba ni na kai shi kara EFCC ba. Ban ma san ya bude asususn ba, har sai da Tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya rubuto min wasika cewa na bada izni su tafi da Mustapha domin yi masa tambayoyin dalilin da ya sa ya bude asusun banki da sunan hukumar FIU.
“Kai ni a lokacin da Mustapha ya yi tabargazar sa ma ban fara aiki a hukumar ba.”
PREMIUM TIMES ta kuma ji yadda Mustapaha da Salihu su ka rika binciken asusun Mambobin Majalisar Dattawa da na Tarayya, ba tare da an ba shi iznin yin hakan ba.
Sai dai kuma su biyun sun ki cewa komai, amma dai Mustapha ya karyata dukkan zargin da ake yi masa.
Discussion about this post