Wani abin tashin hankali da ya auku a wasu kauyukan karamar hukumar Safana dake jihar Katsina shine yadda wasu ƴan bindiga suka afka wasu kauyukan karamar hukumar suka babbake gari guda sukutum, suka kuma cinnawa rubunan adana abinci sama da 50.
Wakilin PREMIUM TIMES da ya ziyarci wannan karamar hukuma sannan yayi tattaki harzuwa ƙauyukan Kabuke, ya ce baya ga wannan ta’adi da aka yi wa mutane, maharan suk kashe mutum 11 a hari.
Shi kansa Dagacin wannan kauye ya arce domin ua tsira da ran sa.
Wani shugaban Al’umma Alhaji Adamu ya shaida wa wakilin PREMIUM TIMES cewa maharan sun dira garin Kabuke tun da misalin karfe 4 na yamma ne.
Ya kara da cewa sai da suka dauki tsawon awa uku suna abinda suka ga dama a cikin wannan kauye. Kafin su fice ne wasu ƴan banga dake kauyukan dake makwabtaka da su suka kawo musu dauki.
Cikin su ne aka kashe mutum 11.
” A kauyen Jar Kuka an kashe mutum ɗaya, Daulai mutum ɗaya, Mai Jaura mutum biyar aka kashe, Kwanar Dutse mutum biyu, sannan a kauyen Kabuke mutum biyu bayan babbake rumbunan abinci sama da 50 da maharan suka yi.
” Waɗannan ƴan bindiga sun yi wa mutanen waɗannan ƙauyuka ta’adin gaske, kuma sun bar su cikin tagumi da Inna-lillahi-wa-inna-ilaihirrajiun.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren ƴan ta’adda babu kakkautawa.
Kusan kullum sai an kai hari wani kauye sannan a yi awon gaba da mutane sai an biya kudin fansa kafin a sake su ko kuma ma a kashe su.
Jihohin Kaduna da Zamfara ma na daga cikin jihohin da ke fama da irin haka.