WUTAR LANTARKI: Gwamnati ta ce a koma tsohon farashi tun na Disamba

0

Ministan Makamashi Saleh Mamman, ya bada umarni Hukumar Raba Hasken Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) cewa ta sanar da kamfanonin saida wutar lantarki su daina karbar sabon farashin kari, su gaggauta komawa tsohon farashi tun na Disamba, 2020.

Babban Kakakin Yada Labarai na Minista, Aaron Atimas ne a bayyana haka a Abuja, cikin wata sanarwar gaggawa da ya fitar a ranar Alhamis.

Y ace komawa kan tsohon farashin ya zama wajibi, domin a samu a cimma dadaddiyar matsayar da ake so a cimma a tattaunawar da ake yi da Shugabannin Kungiyar Kwadago ta Kasa tukunna.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa an fara karya kumallon 2021 da karin kashi 50/100 na kudin wutar lantarki.

’Yan Najeriya sun tashi da jin labarin karin wutar lantarki har na kashi 50/100, watanni biyu bayan an yi karin kudin ba da dadewa ba.

Karin ya zo kwanaki biyar bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa duk wata hukumar gwamnatin tarayya da ta kasa tara kudade masu yawa a cikin 2021, to shugaban hukumar zai ji a jikin sa.

Haka abin ya faru a farkon shekarar 2020, inda aka yi karin kudin wutar lantarki.

Bayan an sake yin wani karin a cikin watan Agusta, sai kuma a cikin Satumba bayan da gwamnati ta ga ana ta sukar karin kudin wuta da na fetur, sai ta bayyana cewa “an yi karin domin ’yan Najeriya su ji dadi.”

Yanzu kuma an sake yin kari har na kashi 50/100, kamar yadda Hukumar Kula da Makamashi ta Kasa (NERC) ta bayyana.

Wannan kari dai NERC ta yi shi ga dukkan kamfanonin sayar da wutar lantarki su 11 na kasar nan. Kenan su kuma za su lafta karin kudin kan kwastomomin su, mai halin biya da kuma talaka.

Shugaban Hukumar Gudanarwar NERC, Sanusi Garba ne ya saw a takardar sanarwar yin karin hannu, wadda aka fitar a ranar 30 Ga Disamba, 2020.

Wannan ya na nufin karin kudin ya fara aiki tuni, tun a ranar 1 Ga Janairu, 2021.

Sanarwar ta ce an yi karin kudin bayan yin la’akari da cewa tsadar rayuwa a kasar nan ta kai kashi 14.9%, sannan kuma zuwa Disamba karshen wata naira 379.4 ake canjar dala.

Dama kuma ko a farkon 2020, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Gwamnati ta bude sabuwar shekarar, waccan ta 2020 da karin kudin wutar lantarki.

Aikin farko da Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatarwa a ranar 1 Ga Janairu, 2020, shi ne karin kudin wutar lantarki har zuwa kashi 78% bisa 100% daga yadda ake shan wutar tun daga 2015.

Share.

game da Author