WURU-WURU: Yadda ’yan cuwa-cuwa su ka toshe bakin matar tsohon minista da naira milyan 75, ladar-ganin-ido -EFCC

0

Hukumar EFCC ta yi wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bayani dalla-dalla yadda aka toshe bakin matar tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Tanimu Turaki da naira milyan 75, na wasu kudin kwangila, alhali ita ba ‘yar kwangila ba ce, kuma ko aikin sisin kwabo ba ta yi wa gwamnatin tarayya ba.

An shaida wa kotun haka a ranar Laraba, kamar yadda ita ma matar tsohon ministan aka hakkake cewa ta amsa cewa ta karbi mudaden.

Jami’an EFCC sun shaida wa Babbar Kotun Tarayya a Abuja cewa Halima Turaki ta karbi naira milyan 75 daga cikin wasu makudan kudaden aikin wayar da kai, wadanda aka karkatar daga Ma’aiakatar Ayyuka na Musamman, a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan, ma’aikatar da mijin ta ya shugabanta.

Bello Hamma-Adama ya tabbatar wa kotu cewa Halima ba ta yi aiki ko na sisin kwabo daga cikin kudin da aka ba ta din ba.

A lokacin da Tanimu Turaki ke Ministan Ayyukan Musamman, Jonathan ya kara masa rikon Ma’aikatar Kwadago a matsayin Ministan Lura da ita ma’aikatar.

EFCC na zargin wala-wala da wuru-wuru na kimanin naira milyan 854 a kan Tanimu Turaki, tsohon Hadimin Musamman na Turaki mai suna Sampson Okpetu da kuma wasu kamfanoni biyu, Samtee Essentials Limited da kuma Pasco Investment Limited.

Amma kuma wadanda ake zargin duk sun ce karya ake yi masu, ba su ci ko kwandala ba.

Hamma-Adama ya shaida wa kotu yadda aka rika karkatar da naira milyan 359 kashi-kashi ana turawa asusun bankunan mutane daban-daban, ciki har da na matar tsohon ministan da kuma na wani kanen sa.

Ya ce a lokaci daya an tura wa Halima naira milyan 45, shi ma Abdullahi Maigwandu, dan uwan ta, an tuRa masa naira milyan 45.

“Daga baya ne aka tura wa Halima Turaki cikon naira milyan 30 ta asusun wani mai suna Abubakar Sani Gude, a asusun sa na bankin Zenith Bank. Daga wannan asusun ne kuma aka tura kudaden cikin asusun Halima Turaki.”

Mai Shari’a Inyang Ekwo ya dage sauraren karar zuwa ranakun 9 da 10 Ga Faburairu.

Share.

game da Author