Tsaro, Yaki da rashawa da inganta tattalin arziki ne za mu fi maida hankali a kai a 2021 – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya sha alwashin kara mikewa tsaye cikin 2021 domin ya fuskanci dukkan matsalolin da su ka sha kan Najeriya a cikin 2020, domin ya magance su.

Ya ce ya ji dukkan korefe-korafen ‘yan Najeriya tare da daukar yakinin cewa a cikin 2021 zai tabbatar dukkan shiyyoyin Najeriya shida sun samu ingantaccen tsaro a kasar nan.

A sakon sa na murnar shiga sabuwar shekara, Buhari ya ce tsaro zai inganta a kasar nan nan ba da dadewa ba, ta yadda har jikokin mu da za a haifa nan da karni na gaba mai zuwa za su ci amfanin tsaron da za a samar ba da dadewa ba.

Sannan kuma ya ce gwamnatin za ta kara dauka majayin goya dimbin matasa a baya, domin samar masu ayyuakn dogaro ta hanyar samun aiki da inganta hanyoyi da dabarun kirkirar kananan sana’o’i.

Buhari ya jaddada cewa shekarar 2021 shekara ce da za mu kara karfafa wa ’yan Najeriya fatan da su ke da shi na ganin an samu Najeriya ta zama kasa kasaitacciya.

A cewar sa, gwamnatin sa za ta maida hankali kan kudirorin ta ko ajandojin ta guda uku, wato tsaro, yaki da rashawa da kuma inganta tattalin arziki.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shekarar 2020 ta kasance wa yan Najeriya cikin tsanani.

Ya bayyana hakan ne a cikin jawabin sa na Sabuwar Shekara da ya karanta kai-tsaye a ranar Juma’a, 1 Ga Janairu, 2021.

Buhari ya ce irin juriya da jimirin daukar dukkan kalubalen da su ka tunkari kasar nan da ‘yan Najeriya su ka nuna, ya tabbatar da cewa a shekarar 2021 al’ummar kasar nan za su kara tashi tsaye domin kara ciyar da kasar nan gaba.

Ya kara da cewa. “yayin da mu ke shiga shekarar 2021 cikin fatan nasara, tilas mu tuna da ’yan’uwan mu da abokan mu da wadanda ba su samu damar tsallake siradin 2020 ba.

Buhari ya yi wa wadanda su ka rasa rayukan su a cikin 2020 addu’a Allah ya rahamshe su, ya kyautata makwancin su.

Da ya waiwaya baya tsawon shekaru 60 bayan samun ’yanci, Buhari ya ce Najeriya ta bai wa masu hangen nesa matukar mamakin yadda ta shanye dafin manyan matsalolin da ta fuskanta a baya da har ta kawo wannan shekara a matsayin dunkulalliyar kasa.

Sai ya ce yin da wasu kasashen su ka rarrabu tsawon shekaru da dama, Najeriya ta ci gaba da kasancewar ta dunkulalliya kam, babu wata girgizar da ta razana ta.

A kan hana ne ya ce babu daren da jemagen Najeriya bai gani ba, don haka wata barazana go gada-gadar ‘yan hauragiya da barababiya ba ta tarwatsa Najeriya ba.

“Baya ga kunci da matsin lambar da tattalin arziki da kuncin rayuwa su ka hau kan jama’a, akwai guguwar zanga-zangar #ENDSARS, wadda matasa su ka tashi tsaye su ka nemi a yi wa aikinn jami’an ‘yan sanda kwaskwarima.

“Wannan zanga-zanga ta yi muni,ta koma tarzoma. Kuma duk da haka, mun saurari koke-koken da wadannan matasa su ka yi. Za a bi hanyoyin da za a share masu hawayen su.” Inji Buhari.

Sai dai kuma shi da kan sa ya yarda cewa shekarar 2020 ta zo da dimbin matsaloli da kalubale iri daban-daban a kasar nan.

Share.

game da Author