A daidai daliban jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria jihar Kaduna na shirye-shiryen komawa karatu gadan-gadan jami’ar ta yi alwashin samar da cikakken tsaro a ciki da wajen jami’ar domin dalibai su samu damai watayawa da yin karatu yadda ya kamata.
Dalibai za su koma makaranta ranar 25 ga Janairu.
Shugaban sashen Samar da Tsaro a jami’ar, Ashiru Zango ne ya bayyana haka a zantawa da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeria ranar Asabar a Zariya.
Domin ganin jami’ar ta wadata tsaro a wannan lokaci da dalibai za su komo karatu, Zango ya ce Jami’ar ta gana da malamai, masu ruwa da tsaki da sauran mutane kan hanyoyin karfafa tsaro a jami’ar da kewaye.
” Mu sanar da dalibai su daina bi ta hanyoyin da ke kusa da dazukan makarantar musamman da dadaddare, sanna kuma duk inda mutane basu cika hada-hada ta wurin ba a rika nesa-nesa da su.
“Mun kuma tattauna da sakarkunan kauyukan dake kewayen jami’an da su taimaka wa jami’an tsaron Jami’ar da bayanan da za su taimaka wajen
samun tsaro a jma’iar da kauyukan na su.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda wasu mahara suka dira Kwatas din jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, a cikin dare suka yi garkuwa da malamin makarantan, matarsa da diyar sa.
Da jami’an tsaro suka bi sawun maharan sai suka saki matar da diyar malamin amma suka tafi da malamin.
A lokacin da wannan abin tashin hankalin ya faru an yi awa 24 da aka sako wasu daliban jami’ar da masu garkuwan da mutane suka yi garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa Zaria.
Discussion about this post