Rundunar ƴan sandan jihar Osun sun kama wata matar aure mai suna Mariam bayan ta kashe wani yaro mai shekara uku saboda tsananin kishi.
Wannan abu dai ya faru ne a kauyen Ede ranar 29 ga Disambar 2020.
Mariam mai shekaru 24 ta bayyana wa jami’an tsaro cewa da gangar ta zuba wa ɗan kishiyar ta maganin kwari wato, fiya-fiya a baki ya sha ya mutu.
Ta ce ta aikata haka ne saboda da tsananin kishi ganin yadda mijinsu ya fi son kishiyarta mahaifiyar yaron.
“Mijin mu ya nuna ya fi son kishiya ta karara a fili saboda ita ce ta haifar masa da namiji.
Mariam ta ce bayan ta sanar wa mijinsu mumunar aikin da ta aikata shine ya dankata ga ‘yan sanda.
PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda wata mata mai suna Hauwa dake unguwar Sagagi rukunin gidaje na Discos, Kano ta kashe ‘ya’yan ta biyu saboda mijinta ya kara aure.
Shugaban Al’umma Ahmed Bello, ya shaida wa mutanen unguwan cewa Hauwa ta aikata wannan mummunar abu ne a lokacin da mijin ke gidan Amaryarsa.
Sannan kuma bayan ta aikata hakan sai ta fita da gudun tsiya. Rahotanni sun nuna cewa ko da makwabta suka yi kokarin kama ta, ta nemi ta illata wadanda suka tsaya a gabanta.
Kawun wadannan yara da ta kashe, ya bayyana wa ‘ƴan sanda cewa tunda mahaifin yaran ya ƙara mata zaman lafiya ya ƙare a wannan gida, bala’in yau dabam da na gobe bam.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce zata cigaba da bincike akai.
Discussion about this post