Jam’iyyar APC ta yi Allah-wadai da jam’iyyar PDP don saboda ta soki gwamnatin Shugaba Muhamadu Buhari.
APC dai a ranar Talata ta fayyace wasu abubuwan da ta kira manyan munanan ayyukan da PDP ta shimfida a doron Najeriya.
Yayin da PDP ta shafe shekaru 16 ta na mulkin Najeriya, daga 1999 zuwa 2015, ita kuma APC ta karba daga 2015 zuwa yau.
Yayin da ’yan Najeriya da dama ke ganin cewa babu wani bambanci tsakanin PDP da APC yanzu haka, shi kuma sakataren riko na APC na ganin cewa biri bai yi kama da mutum ba, domin ba kamannin su daya ba.
“Lallai ma jam’iyyar PDP ba ta da kunya da darajar da har za ta ma rika kwatanta kan ta da jam’iyyar APC.” Haka Udodehe ya bayyana.
“Maimakon PDP ta lullube kan ta a daina ji da ganin ta saboda abin kunyar da ta tafka a kasar nan, sai ta ci gaba da tona wa kan ta asiri, ta na tunatar da mu zamanin da kasar nan ta samu dimbin arziki, amma duk aka ragargaza shi karkaf.”
Daga nan sai ya yi wa PDP gorin wasu makudan kudaden da su ka salwanta a Babban Bankin Najeriya, CBN kuma kudaden makaman yaki da ta’addancin da aka danne a lokacin PDP.
Ya kuma ce akwai wasu bilyoyin dalolin da aka kasafta domin sayo makaman yaki da Boko Haram, amma duk manyan ‘yan PDP su ka daka wasoson kudaden.
“PDP ta rika ragargaje kudaden jama’a wajen biyan matsafa da ‘yan bori, malamai da ‘yan tsibbu da sarakunan gargajiya, domin cin zaben 2015.” Inji shi.
Ya kara da yin bayanin yadda gwamnatin PDP ta rika shafe wata da watanni ba tare da an iya biyan albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya da jihohi ba, har sai da gwamnatin Buhari ta hau sannan ta saisaita al’amurra.