Tabarbarewar da fannin kiwon lafiyar Najeriya ya yi yafi dacewa mahukunta su maida hankali a akai ba kokawar siyan rigakafin Korona ba – Bill Gates

0

Fitaccen Attajiri kuma gogan mai yi wa kasashe hidima ta hanyar basu tallafi musamman a fannin kiwon Lafiya, Bill Gates ya yi kira ga mahukunta a Najeriya da su mai da hankali wajen inganta fannin kiwon lafiyar Kasar maimakon kokawar siyan rigakafin Korona.

Gates ya fadi haka ne ranar Talata da yake ganawa da manema labarai.

Ya ce kamata ya yi Najeriya ta yi amfani da kudadenta wajen inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko domin talakawanta musamman yara kanana su samu kiwon lafiya nagari ba narka kudi ba wajen mallakar ruwan rigakafin Korona ba.

Gate ya bayyana haka a matsayin shawarar sa ga mahukunta a kasar ganin yadda gwamnatin ta ware naira biliyan 400 domin siyo rigakafin Korona domin ‘yan kasar wanda ba ma duka za su samu da wannan kudi da gwamnati ta ware ba.

Najeriya za ta siya kowane kwalban maganin rigakafin akan dala $8.

Idan ba a manta ba a Disambar 2020 ministan lafiya Osagie Ehanire ya bayyana wa majalisar dattawa cewa gwamnati za ta kashe naira biliyan 156 a shekarar 2020 da kuma wasu naira biliyan 200 a shekaran 2021 wajen yi wa mutane rigakafin cutar Korona a kasar nan.

Gates ya ce Najeriya na cikin kasashen duniyan da kamfanin hada magunguna na GAVI za ta tallafawa da maganin rigakafin Korona, ya ce ta hakura ta jira maimakon narka biliyoyin naira wajen siyan maganin, fannin lafiyar kasar ya fi bukatar wadannan kudade.

Idan haka da gaske ne za a bata gudunmawar maganin nan gaba, me yasa Najeriya ba za ta iya jira ta karbi tallafin GAVI a maimakon siyo maganin a farashin mai tsada ba. ” Maimakon haka sai ta saka kudin wajen inganta fannin lafiyar kasar.”

Ehanire ya ce gwamnati ta kammala shiri tsaf domin karban kwalaban maganin rigakafin cutar guda 100,000 a karshen watan Janairu.

Ya kuma ce kamfanin Gavi ta yi alkawarin tallafa wa Najeriya da kwalaban maganin miliyan 42.

Gates ya kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dauki darasi a yakin da take yi da Korona domin shirya wa wata annobar koda ta bayyana nan gaba.

Share.

game da Author