SSS sun yi zargin ana rura wutar rikicin addini a Najeriya

0

Jami’an Tsaro na Farin Kaya (SSS ko DSS), sun yi zargin wasu na kulle-kullen rura wutar fitinar addini a wasu sassa na kasar nan.

Hukumar ta SSS ta yi wannan bayani a cikin wata takardar sanarwa da Kakakin DSS din mai suna Peter Afunanya ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

Afunanya ya lissafa wasu jihohi 12 da ya ce a cikin su ne ake kokarin rura wutar rikicin addinin.

Sannan ya yi kira ga jama’ar Najeriya su guji kalamar rarrabuwar kawuna.

“Hukumar Tsaro ta DSS ta sanar da jama’a cewa su yi kaffa-kaffa da masu neman tayar da fitina ta hanyar amfani da wasu mugaye daga wajen domin su haddasa wutar rikici a cikinn kasar nan.

“Jihihin da su ke kokarin ballo wa ruwa sun hada da Sokoto, Kano, Kaduna, Filato, Rivers, Oyo, Lagos da kuma wasu Jihohi a Kudu Maso Gabas.

“Nufin su shi ne su haddasa rikicin addini ta hanyar amfani da mabiyan su domin su kai wa wasu wuraren ibada hari da kuma hari kan wasu shugabannin addinai da sauran su.”

“Don haka ana shawartar ‘yan Najeriya su yi kaffa-kaffa Da masu wannan mummunan nufi.”

Yayin da ya yi kira ga sauran bangarorin jami’an tsaro su yi aiki tare daomin wanzar da zaman lafiya. Afunanya ya yi kira ga jama’a su kai rahoton duk wani da aka gani ya na neman tayar da zaune tsaye.

Wannan takarda da SSS ta fitar ta zo ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara ruruwa a kasar nan.

Abubawan Da Su Ka Biyo Bayan Shiga Sheakar 2021:

Kalaman Bishof Hassan Kukah a kan gwamnatin Shugaba Muhammadun Buhari sun tayar da hanayaniya a social midiya. Yayin da wasu ke ganin gaskiya ya bayyana, wasu da dama na ganin cewa kamar ya taba ruhin wani addini ne a fakaice. Tabbas kalaman na Kukah sun haddasa rabuwar kawunan ra’ayi da na addini a cikin kasar nan.

A Kano ma hayaniya ta kaure a soshiyal midiya, a cikin kwanakin nan biyu, tun bayan bullar wani faifan murya wadda ake ikirarin wani babban malami ne mazaunin garin da ya yi ikirarin cewa, idan su ka samu dama za su iya kashe wani fitaccen malami da ke Kano.

Furucin na sa ya sa magoya bayan malamin da aka yi zargin da shi ake, su na cewa idan aka taba malamin na su, to za su yi ramuwar gayya.

Har yanzu dai malamin da aka rika bayyana cewa muryar wanda ya yin ikirarin zai yi kisan ta sa ce, bai fito ya karyata cewa ba shi ba ne.

Kisan wasu makiyaya cikin karshen makon jiya a yankin Kudu maso Yamma ya tayar da jijiyar wuya, inda wani bangare na kasar nan ke ganin cewa an kashe wadanda ba su da alaka da masu garkuwa da mutane.

Hakan ya sa wani bangare na kasar nan ya rika daga babbar murya a soshiyal midiya, ya na ganin cewa an kafa kungiyar tsaro ta Amotekun, wadda ake zargin ta yi kisan da nufin far wa mazauna yankin wadanda ba ‘yan kabilar ta ba.

A yankin Kudu maso Gabas ma bullar wani bidiyo da ke nuna ana yi wa wasu kabilun da ke zaune yankin korar-kare ko a ce korar-wulakanci, ya tayar hayaniya a soshiyal midiya.

Duk wadannan al’amurra sun faru daga ranar 1 Ga Janairu zuwa ranar 10 Ga Janairu.

Tuni dai jama’a ke ta kiraye-kirayen ya kamata jami’an tsaro da gwamnatin tarayya su tashi tsaye su shiga tsakani.

Share.

game da Author