Kodineton yada labarai na rundunar Sojojin Najeriya John Enenche ya bayyana cewa sojojin saman Najeriya sun yi ragaraga da ‘yan bindiga dake addabar matafiya a titin Abuja-Kaduna ranar Lahadi.
Enenche ya ce adaidai jiragen yakin na shawagi a sama sai suka hango wasu mahara akan babura suna kokarin nausawa cikin dajin yankin Neja.
” Daga nan ne fa suka rika yi musu aman wuta daga sama, suma maharan sun rika kokarin harbin jiragen daga kasa sai daian fi karfinsu. Da yawa daga cikin su sun mutu, wasu kuma da dama sun arce da rauni a jikin su.
A karshe Enenche ya ce sojojin sama za su ci gaba da kai wa mahara irin wannan samame ta samam har sai sun gama da su.