Sojoji sun kashe Boko Haram da dama a Barno

0

Kodinatan yada labaran rundunar Sojojin Najeriya, John Enenche ya bayyana cewa dakarun Najeriya dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ sun yi nasarar kashe wasu ƴan Boko Haram da dama a jihar Barno.

Enenche ya dakarun sun samu wannan nasara ne a kauyen Wamdeo-Chul bayan sun hada karfi da rundunar sojojin sama.

“Yayin da sojojin operation lafiya dole ke ragargazar Boko Haram a ƙasa rundunar sojin sama kuma na yi musu luguden wuta ta sama.

“Da dama sun mutu wasu sun ji rauni a jikinsu sannan an kona motocin bindigogi biyu da maharan ke amfani da su. Duk da haka ba a tsaya nan ba domin jiragen yakin sun ci gaba da yi musu ambaliya albarusai da bamabamai daga sama sai sai da suka ga bayan su.

PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda wasu mahara da ake zaton Boko Haram sun kai hari garin Geidam a jihar Yobe ranar Laraba.

Share.

game da Author