Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shekarar 2020 ta kasance wa yan Najeriya cikin tsanani.
Ya bayyana hakan ne a cikin jawabin sa na Sabuwar Shekara da ya karanta kai-tsaye a ranar Juma’a, 1 Ga Janairu, 2021.
Buhari ya ce irin juriya da jimirin daukar dukkan kalubalen da su ka tunkari kasar nan da ‘yan Najeriya su ka nuna, ya tabbatar da cewa a shekarar 2021 al’ummar kasar nan za su kara tashi tsaye domin kara ciyar da kasar nan gaba.
Ya kara da cewa. “yayin da mu ke shiga shekarar 2021 cikin fatan nasara, tilas mu tuna da ’yan’uwan mu da abokan mu da wadanda ba su samu damar tsallake siradin 2020 ba.
Buhari ya yi wa wadanda su ka rasa rayukan su a cikin 2020 addu’a Allah ya rahamshe su, ya kyautata makwancin su.
Da ya waiwaya baya tsawon shekaru 60 bayan samun ’yanci, Buhari ya ce Najeriya ta bai wa masu hangen nesa matukar mamakin yadda ta shanye dafin manyan matsalolin da ta fuskanta a baya da har ta kawo wannan shekara a matsayin dunkulalliyar kasa.
Sai ya ce yin da wasu kasashen su ka rarrabu tsawon shekaru da dama, Najeriya ta ci gaba da kasancewar ta dunkulalliya kam, babu wata girgizar da ta razana ta.
A kan hana ne ya ce babu daren da jemagen Najeriya bai gani ba, don haka wata barazana go gada-gadar ‘yan hauragiya da barababiya ba ta tarwatsa Najeriya ba.
“Baya ga kunci da matsin lambar da tattalin arziki da kuncin rayuwa su ka hau kan jama’a, akwai guguwar zanga-zangar #ENDSARS, wadda matasa su ka tashi tsaye su ka nemi a yi wa aikinn jami’an ‘yan sanda kwaskwarima.
“Wannan zanga-zanga ta yi muni,ta koma tarzoma. Kuma duk da haka, mun saurari koke-koken da wadannan matasa su ka yi. Za a bi hanyoyin da za a share masu hawayen su.” Inji Buhari.
Sai dai kuma shi da kan sa ya yarda cewa shekarar 2020 ta zo da dimbin matsaloli da kalubale iri daban-daban a kasar nan.