SHARHI: Dalilai 8 Da Kasafin 2021 Ya Cancanci Jibgewa A Kwandon Shara

0

Ganin yadda marubucin ya kwalailaice cewa ba a auna Kasafin 2021 a kan mizanin awon rayuwar talakawa da bunkasa kasa ba, hakan ya sa PREMIUM TIMES HAUSA ta bi rubutun na sa dalla-dalla ta tsakuro abin da ya kamata masu karatun Hausa su san yadda kasafin zai karkare a karshen shekara.

1. Najeriya za ta shafe shekara daya cur ta na neman bashin naira tiriliyan 5.02, wadanda sai da su za a iya aiwatar da ayyukan kasafin 2021. Kenan kashi 40% bisa 100% na Kasafin naira tiriliyan 13.58 bashi ne za a ciwo, idan har ma an samu wanda zai bayar da bashin.

2. Kasashe manya su na yin kasafin su na shekara ta yadda zai amfani wasu kasashe masu yawa. Misali za a yi la’akari da me za a samar a ahekarar wanda wadancan kasashen tilas sai sun zo sun saya? Kamar makamai da sauran su.

A kasafin 2021 na Najeriya babu abin da za a samar wanda tilas sai Togo, Chadi, Ghana da sauran kasahen birjik sun shigo sun saya tilas.

3. Kasafin naira tiriliyan 13.58 ba wata tsiya ba ce a Kasa mai yawan al’umma kamar mutum milyan 200. Saboda darajar naira ta lalace a idon kudaden kasashen waje.

Naira tiriliyan 13.58 daidai ta ke da Dala biliyan 34 kacal.

4. Cikin Naira biliyan 13.58, za a kashe naira tiriliyan 5 wajen biyan albashin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (wato kashi 40% bisa 100% na kasafin).

Hakan na nufin daga cikin naira tiriliyan 7 da ake hasashen samu a matsayin kudin shiga, to naira bilyan 5 duk a biyan albashi za su tafi kenan.

Shin a ina albarka ko bunkasa tattalin arzikin kasa ya ke a cikin kasafin 2021?

5. Kasafin naira tiriliyan 13.58, amma za a kashe naira tiriliyan 5 cur ga Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da ba su wuce su MILYAN 2 ba!

Za a kashe naira bilyan 134 kan Majalisar Dattawa da ta Tarayya su kamar 500 kacal da ma’aikatan su.

Sauran naira tiriliyan 8 ne za a kashe kan sauran ‘yan Najeriya arankatakaf din mu.

Hakan ya na nufin Dala 80 kenan za a kashe kan kowane dan Najeriya a tsawon shekara daya.

Idan kuwa aka kammale kasafin wuri daya naira tiriliyan 13.58, za a ga cewa a cikin shekarar 2021, za a kashe wa kowane dan Najeriya Dala 170 kakaf a kan ilmi, tsaro, harkar ‘yan sanda, lafiya da sauran bangarori.

6. Yayin da kasashen irin su Afrika ta Kudu ke aiwatar da Kasafin Ciyar Da Kasa Gaba, ciki har da kashe kudaden wajen koya wa yara ‘yan firamare dabarun mutum-mutumin ‘robot’, mu a kasafin mu ana jawabi sai dai ka ji ana batun za a gyara titin Bidda ko titin Jalingo. Iyakar kololuwar ci gaban mu keman.

7. Idan ka kalli kasafin 2021, za ka ga cewa kacokan kasafin ne da kawai zai amfani manyan ‘yan siyasa da manyan ‘yan kwangila wadanda ake bai wa odar sayo wa gwamnari wasu kayayyaki.

Talaka zai iya amfana, amma inda zai amfana din, bai wuce ya tsinci guntun tuwon da ya fado daga kan teburin da manyan ‘yan siyasa su ka yi watandar tuwon walimar kasafin 2021 ba. Shikenan!

8. Duk fa maganar Kasafin 2021 da ake yi, babu ko sisi a kasa ajiye. Sannan duk tsatsuniya ce, domin tsawon shekaru 15 da su ka gabata, a kasar nan ba a taba aiwatar da sama da kashi 40% bisa 100% naanyan ayyukan da aka ce za a yi a kasafin kowace shekara ba.

Kasafin 2021, gudun tsira ko dai tuma tsalle wuri daya?

Share.

game da Author