Wata likita da ta kware wajen sanin amfanin ‘ya’yan itatuwa da sassaken itatuwa wajen yin amfani dasu don warkar da cututtuka, Hetal Jariwala ta karyata cewa da ake yi wai cin kwakwa na sa a kamu da tari.
Shima likitan wani asibiti a Ibadan Oluwaseun Ige ya ce kwakwa na dauke da sinadarin dake warkar da mura ko tari amma ba ya saka shi ba ko kuma ya kara shi ba.
Ya ce kwakwa na dauke da sinadarin Vitamin C, potassium, calcium, copper, phosphorus, chlorine, magnesium, sulphur da sodium wanda ke inganta kiwon lafiyar mutum.
Wadannan likitoci sun fadi haka ne bayan wani mutum mai suna Freeman ya rubuta a shafinsa na tiwita cewa cin kwakwa na kawo tari.
Ga amfani kwakwa 12 a jikin mutum.
1. Ruwan kwakwa na warkar da ciwon kai. Idan mutum ya sha a lokacin da ya ke ciwon kai zai rika samun sauki.
2. Kwakwa na kawar da cutar daji musamman dajin dake kama dubura da nono.
3. Yana kawar da cutar siga wato ‘Diabetes’
4. Kwakwa na kawar da ciwon kafa ( Sanyin Kashi) wato ‘Arthritis’
5. Yana kara karfin ido.
6. Yana kaifafa kwakwalwa.
7. Shan ruwan kwakwa na rage kiba a jiki.
8. Kwakwa na kara karfin gaban namiji.
9. Yana gyara fatar mutum.
10. Yana kara tsawon gashi.
11. Shan ruwan kwakwa na kare mutum daga kamuwa da cutar koda da huhu.
12. Yana hana tsufa da wuri
Discussion about this post