Babbar Kotun Jihar Ekiti ta daure Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda rai-da-rai a kurkuku, bisa kama shi da laifin sayen motar da ya tabbatar ta sata ce, tun kafin ya fara ciniki.
An daure Okubo Aboye rai-da-rai a kurkuku saboda sayen mota daga hannun masu garkuwa da mutane.
A ranar Litinin kotu ta daure shi tare da bakaniken da ya sayar masa da motar mai suna Niyi Afolabi.
Kwafen tuhumar da aka yi masa na dauke da bayanan cewa an kama Aboye da laifin sayen motar sata, samfurin Toyota Hilux da ya saya daga hannun masu garkuwa da mutane, ta hanyar dillancin Afolabi, wanda shi kuma bakanike ne.
An aikata laifin tun a ranar 9 zuwa 19 Ga Mayu, 2005 a unguwar GRA, Ado Ekiti.
A lokacin masu garkuwa da mutane sun je dauke da bindigogi su ka tafi da wani mai suna Moses Ajogri, mai shekaru 40.
Bayan sun yi masa fashin motar sa Toyota Hilux mai lamba APP 509 BK.
Mai gabatar da kara ya ce laifin ya saba wa Sashe na 346(2), 1(2) da kuma Sashe na 5 na Dokokin Jihar Ekiti ta 2012 da ma wasu dokokin fashi da makami na 2004.
Mai Shari’a John Adeyeye ya ce idan har kotu ba ta koya wa mataimakin kwamishinan ‘yan sandan darasi ba, to abin zai zubar da darajar kotu.
Mai Shari’a Adeyeye ya ce hujjojin da aka tabbatar a gaban kotu sun nuna cewa dan sandan ya san motar fashin ta aka yi, haka shi ma bakaniken ya san motar ta sata ce.
“Na same ku da laifin sayen kayan sata. Kuma hujjoji sun nuna kun sa kayan da masu fashi da makami su ka sato ne.Don haka na yanke maku hukuncin daurin rai-da-rai a kurkuku.”