Kakakin jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu, Tunde Rahman, ya karyata raderadin da ke ta yayyadawa a kafafen sada zumunta a yanar gizo wai Tinubun na fama da Korona, yana can kasar waje ana duba shi.
Rahman ya ce wannan magana babu kamshin gaskiya a cikinta.
” Sau 15 ana yi wa Tinubu gwajin Korona ba a taba ganinta a jikin sa ba.
” A Duk lokacin da yayi tafiya ko kuma yayi mu’amula da mutane, yakan kai kan Sa ayi masa gwajin cutar. Ba a taba ganin cutar a jikin sa sau 15 kenan ana duba shi.
” Sannan kuma ba kamar yadda ake ta yadawa wai yana kwance a asibiti a kasar Faransa ana duba shi ba, gaskiyar magana ita ce Tinubu na kwance ne a kasar Birtaniya yana hutawa.
A karshe Rahaman ya ce Tinubu mutum ne mai biyayya ga ka’idojin Korona, amma kuma duk da haka baya wasa da yin gwaji a duk lokacin da ya cakudu da jama’a.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 576 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –277, FCT-90, Oyo-51, Nasarawa-49, Sokoto-23, Anambra-14, Bauchi-11, Imo-11, Kano-11, Edo-10, Plateau-10, Ogun-9, Osun-5, Jigawa-3, Rivers-2
Yanzu mutum 89,163 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 74,789 sun warke, 1,302 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 13,072 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Juma’a, mutum 1,074 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Kaduna, Rivers, Gombe, Kano da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.