Shugabar Kwamitin shirin burin ci gaba mai dorewa (SDG) na majalisar Dattawa, Hajiya Aisha Dahiru Ahmed (Binani) ta jinjina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan saka hannu da yayi akan kudirin Kafa Jami’ar Modibbo Adama dake jihar Adamawa.
Sanatar wacce ita ce ta bijiro da wannan kudiri a majalisar Dattawa ta ce, yanzu jami’ar za ta gudanar da ayyukan ta kamar yadda sauran manyan jami’o’in kasar nan ke gudanarwa.
Sannan kuma ta ce wannan kudiri zai samarwa dinbin matasa guraben karatu a jami’ar.
” Abin a yaba ne da farin ciki matuka amincewar da Shugaban kasa ya yi wa wannan kudirin har ya saka hannu. Shugaba Buhari ya rattaba hannu a wannan kudirin sauya MAUTECH zuwa cikakkiyar jami’ar da za a dalibai za su rika karatun aikin likitanci da ilimin zamantakewar jama’a da ilimin gudanarwa da sauransu.
” Hakan ya tabbatar da cewa jami’ar za ta rika tafiyar da al’amuran karatun ta kamar yadda sauran jami’o’in kasar nan keyi,a fannonin koyan aikin likitanci da ilimin zamantakewa da dai sauransu.
” A madadin mutanen jihar Adamawa da jihar Taraba, muna mika godiyar mu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan wannan abu da aka yi mana, ba za mu taba mantawa da wannan karamci da nuna kauna da son cigaban al’ummar mu da aka nuna mana ba.
” Yin haka zai kara wa matasan mu kwarin guiwar shiga makaranta domin samun ilimi mai nagarta a koda yaushe musamman a wannan lokaci da muke ciki.
” Baya ga zama a kan gaba wajen karatun fasaha, sabuwar dokar za ta ba jami’ar Modibbo Adama damar bunkasa ta hanyar fadada kwasa-kwasan ta da kuma samar da dama masu yawa ga matasa.
Bayan haka Sanata Aisha ta ambato wasu dalilai da ya sa ta kirkiro wannan kudiri kuma ta jajirce wajen ganin ya kai ga wannan mataki da ya kai, tana mai cewa ta yi haka ne domin a samar wa matasan jihohin Adamawa da Taraba ilmi mai nagarta da kuma don mutanen yankin Arewa Maso Gabas.
” Neman a samu dacewa da sauya MAUTECH zuwa cikkakiyar jami’a ya samo asaline tun ina majalisar Tarayya, wato majalisar wakilai a zango na 7, lokacin da nake wakiltar Yola ta Arewa, Yola ta Kudu, da Karamar Hukumar Girei a majalisar.
” Buri na kuwa shine in ga jami’ar MAUTECH ta daukaka zuwa cikakkiyar jami’a da za ta rika gudanar da kwasa-kwasai irin, koyon aikin likitanci da manya-manyan kwasa-kwasai, kuma gashi Allah ya sa an dace yanzu.
Takardar neman a kafa makarantar likitanci cikin gaggawa a jami’ar Fasaha ta Modibbo Adama, Yola da kuma daukaka darajar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, dake Yola, zuwa Asibitin Koyarwar Jami’a an gabatar da ita a gaban Majalisar Dattawa sannan daga baya Sanata Aishatu Dahiru Ahmed Binani ta gabatar da shi a matsayin Kudirin mai taken ‘Dokar Jami’ar Modibbo Adama don karatu na farko a gaban Majalisar Dattawa. Daga baya an sanya Dokar don karatu na biyu.
” Domin asamu nasara akan haka an gudanar da tarukka na musayan ra’ayoyi da jin ra’ayoyin mutane game da kudiri. Kuma duk wadanda suka halarci zaman sun amince da a tabbatar da wannan kudiri ya zama doka ganin alfanun da ke cikin wannan kudiri.
A karshe dai, majalisar dattawa ta amince da kudirin sannan kuma ta aika wa shugaba Buhari domin ya rattaba hannu akai.