Rushe jihohi a kirkiri shiyya-shiyya ba zai amfani Najeriya ba -Jega

0

Tsohon Shugaban INEC, Attahiru Jega ya bayyana cewa babu abin da Najeriya za ta amfana idan aka sauya fasalin Najeriya, aka rushe jihohi aka maye gurbin su da shiyya-shiyya.

Jega yace sauka fasalin kasar da zai kai ga rushe jihohi, zai yi wa Najeriya illa, maimakon a ci moriyar sa kamar yadda aka dade ana tunanin zai yiwu.

Jega ya yi wannan bayani ne a wurin taron Daily Trust karo na 18, da ake shiryawa duk shekara.

An gudanar da taron a ranar Alhamis a Abuja.

Bayan samun ‘yanci dai Najeriya ta yi tsarin mulkin yanki, inda aka shata ikon kasa ga Arewa, Kudu da Yamma.

Amma daga baya an kirkiro yankin tsakiyar yamma, domin a magance rikice-rikicen kabilancin da ya ki ci, ya ki cinyewa a yankin, a wancan lokacin.

Lokacin mulkin Yakubu Gowon ne aka karkasa yankunan zuwa jihohi 12, domin dakile rikice-rikicen kabilancin da su ka rika tashi nan da can, a cikin 1967.

An rika kara kirkiro jihohi, har dai a cikin 1996, su ka kai jihohi 36.

Sai dai kuma an dade ana fafutikar a koma tsarin mulkin shiyya-shiyya a kasar nan, musamman kiraye-kiraye daga wasu kungiyoyi da sassan da ke korafin ana danne masu hakki a rabon arzikin kasa.

Sai dai Jega ya kara da cewa zai yi wahala a sake fasalin kasar nan, saboda jihohi a yanzu babu wadda za ta amince ta mika karfin ikon ta ga gwamnatin yanki.

Sannan kuma ya ce kokarin komawa ga tsohon salon mulkin, zai kara rura wutar fitina ko zaman dardar a tsakanin kalilun kasar nan.

“Saboda idan aka duba za a ga cewa kirkiro jihohi da aka yi ya magance korafe-korafen maida kananan kabilu saniyar-ware a yankuna da yawa na kasar nan.” Inji Jega.

“Duk da ana kara samun korafe-korafen danniyar kananan kabilu idan ma ana ci gaba da kirkiro sabbin jihohi, to komawa tsohon tsarin shiyya-shiyya zai kara dagula al’amurra kwarai a kasar nan.

“Kuma jihohin da su ka dandana dadin mulki a ‘yancin cin gashin kai, ba za mu amince a sake tattara su wuri daya a karkashin wata gwamnatin yanki ba. Ba ma zai yiwu su amince ba.”

“Na yarda a zancen cewa yawancin jihohin nan 36 ba su iya ciyar da kan su, kuma ba s u iya tsayuwa da kafafun su, har sai sun dogara da gwamnatin tarayya. To amma akwai hanyoyin da za a iya shawo kan wannan matsala.

Jega ya ce za a iya magance matsalolin jihohi ta hanyar sa-ido kan kudaden da ake tura masu, kashe rashawa baki daya, kirkiro hanyar kudaden shiga a cikin jiha da sauran hanyoyin hana almubazzaranci da dukiyar jama’a a cikin jihohi.

Saidai kuma tsohon shugaban Kungiyar Igbo Zalla, Ohaneaze Ndi Igbo, John Nwodo, ya ce akwai bukatar a koma tsarin shiyya-shiyya, domin dokar Najeriya ko kuma tsarin mulkin Najeriya na 1999, mutum 47 ne kacal su ka kirkiro kundin tsarin mulkin, wadanda 40 daga cikin su duk sojoji ne, a karkashin mulkin Abdulsami Abubakar.

Nwodo wanda a lokacin da aka kirkiro Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, shi ne Ministan Yada Labarai a karkashin gwamnatin Abdulsalami Abubakar, ya bayyana cewa bai taba ganin daftarin tsarin mulkin ba kafin a buga shi ya zama kundi.

Ya ce kuma har yau bai san wanda ya buga kundin tsarin mulkin ba, a matsayin sa na Minista wanda aikin sa shi ne rarraba kwafe-kwafen kundin tsarin mulkin ga kasar nan.

“Kawai a tashi a sake fasalin tsarin mulkin kasar nan, saboda sahihin kundin dokar tsarin mulkin Najeriya, shi ne wanda aka kirkiro tare da wakilcin dukkan kabilun Najeriya, a 1960 da 1963, amma ba na 1999, wanda mutum 40 da kadan kadai su ka rubuta. Cikin su ma mutum 40 duk sojoji ne.”

Share.

game da Author