RIKICIN YARABAWA DA FULANI: Gwamnonin jihohin Yarabawa za su zauna da shugabannin Miyetti Allah

0

Yayin da wa’adin kwanaki bakwai da Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya bai wa Fulani makiyaya su fice daga dazukan Jihar Ondo ke karatowa, gwamnonin jihohin Yarabawa shida sun amince za su yi zaman tattaunawa da shugabannin kungiyar Miyetti Allah na Najeriya a Akure.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa za a yi zaman ne domin tattauna matsala wa’adin na kwanaki bakwai da aka ba makiyaya domin su fice daga dazukan na jihar Ondo.

Ana sa ran za a tattauna yadda za a kawo karshen yawan kashe-kashen rayukan da ake yi tsakanin makiyaya da manoma a dukkan jihohin Kudu maso Yamma baki daya.

Gwamnaonin da za a yi zaman da su sun hada na Rotimi Akeredolu (Ondo), Seyi Makinde (Oyo), Kayode Fayemi (Ekiti), Dapo Abiodun (Ogun), Gboyega Oyetola (Osun) da kuma Babajide Sanwo-Olu (Lagos).

Kakakin Yada Labarai na Gwamnan Jihar Osun, Ismail Omipidan ne ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa, “tabbas akwai wannnan taron da za a gudanar a ranar Litinin a Akure, babban birnin Jihar Ondo.”

PREMIUM TIMES ta buga yadda wani shugaban matasa mai suna Sunday Igbolo ya bada irin wannan wa’adin korar Fulani makiyaya a Jihar Oyo, abin da ya haifar da tashin hankalin da har aka kona gidaje da dukiyoyin Sarkin Fulanin Oyo.

Tuni da Sufeto Janar na ’Yan Sanda Mohammed Adamu ya bada umarnin a yi bincike.

Yayin da wasu lauyoyi su ke ganin cewa Sunday ba shi da ‘yancin korar Fulanin, matasan yankin na cewa su na da ‘yancin kare kan su.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Miyetti Allah sun nemi a kamo Sunday Igboho mai rura fitinar korar makiyaya.

Kungiyar Kare Muradin Fulani Makiyaya, Miyetti Allah, ta yi kira a gaggauta kama dan rajin kafa kasar Yarabawa mai suna Sunday Igboho.

Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah na Jihar Oyo, Ibrahim Jiji ne ya bayyana haka ga manema labarai a Ibadan babban birnin Jihar, inda ya kara hakkakewa cewa Fulani makiyaya fa ba mabarnata ba ne.

“Dukkan mu dai ‘yan Najeriya ne. Mu na kaunar kokarin da Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde ke yi wajen fitowa karara ya na fadin gaskiya. Mutanen ba su zaune lafiya, su na cikin tashin hankali, wasu ma sun gudu sun bar gidajen su.

“Mu na so a yi wa Sarkin Fulani adalcin dangane da barnar da aka yi masa a gida. Dukkan wadanda su ka yi masa barnar kona masa gidaje da dukiyoyi dole a kama su a hukunta su. Saboda ba su fi gwamnati karfi ba. Wane ne Sunday Igboho, kuma ta yaya aka yi har ya fi karfin gwamnati?

“Na sha fada cewa a cikin kowace kabila akwai mabarnata, ba wai sai a cikin Fulani kadai ba. Wadanda a yanzu ake gallazawa ba su ne masu laifin da ke addabar jama’a din ba. Wadanda ake kora a yanzu su ne fa ke zaune alfiya da mutane. Ya kamata gwamnati ta yi dukkan kokarin da za ta yi domin ta tabbatar zaman lafiya ya dawo a yankin Ibarapa.”

Shi dai Igboho shi ne ya ja zugar wasu matasa su ka kai wa Fulani farmaki a Ibarapa.

Sai dai kuma Kakakin Fadar Shugaban Kasa Garba Shehu, ya ce Shugaba Muhammadub Buhari ya umarci Sufeto Janar na ‘Yan sanda Mohammed Adamu ya sa a kama Sunday Igboho.

Sai dai kuma Kakakin Yan sandan Najeriya Frank Mba da na Jihar Oyo Olugbengba Fadeyi ba su amsa kiran PREMIUM TIMES ba, domin jin inda aka kwana.

Za A Yi Bala’i A Kasar Nan Idan Aka Kama Igboho –Matasan Yarabawa.

Tuni da Yarabawa su ka tashi haikan a kungiyance su na cewa idan aka kama Sunday Igboho, to za a yi bala’i a kasar nan.

Haka shugaban kungiyar Matasan Yarabawa Olalekan Hammed ya bayyana.

Ya ce matasan yankin Ibarapa da ma wasu matasana Yarabawa ba za su bari a kama dan uwan su ba.

Share.

game da Author