“Na fara sanin Sunday Igboho tun cikin 2009, lokacin da Kotun Koli ta ce a sake wasu zabuka a wasu mazabu, a zaben Gwamnan Jihar Ekiti, tsakanin Segun Oni na PDP da kuma Kayode Fayemi na ACN.
“Lokacin an rigaya an bayyana Oni ne ya ci zaben, amma ACN ta kai kara, kotu ta ce a sake zabe a wasu mazabu.
“Na bada shawara cewa ko ta halin kaka mu samu kudin da za mu sallame su idan ma sun zo din, don kada su tayar mana da yamutsi.
“Lokacin jam’iyar PDP na mulki, ko ta halin kaka ba ta so jihar Ekiti ta subuce mata. Shi kuma Tinubu ya yi rantsuwar-kaffarar sai ACN ta ci gwamnan Ekiti.
“Haka dai na tara gaggan ‘yan-rugumutsin tayar da rudanin zabe irin su Ade Basket a Akure da kuma Fada Geri a Ondo. Har yarjejeniya na rubuta, su ka sa hannu cewa ba za su sa yaran su tayar da rudani a wurin zabukan ba. Su ka ce ko zuwa ma ba za su yi ba.
“Babbar matasalar mu a lokacin shi ne Sunday Igboho, wanda mu ka ji labarin cewa wani garnakakin dan iska ne da wani sanata daga Osun ya dauko sojan-haya domin kawai ya tayar da hankali a zaben Ekiti a 2009.
“Shi kuma Bola Tinubu ya ce min ko ta halin kaka sai mun samu Sunday Igboho din nan na kai masa shi.
Ganawa Ta Da Gogarma Sunday Igboho Cikin Wani Otal:
Kwanaki shida kafin zabe, sai na yi sa’a na samu wani da ya ke da lambar wayar Sunday Igboho. Na kira shi, kuma nay i sa’a ya dauka.
“Na shaida masa cewa mu hadu a wani wuri a Ibadan. Mu ka hadu a wani otal da ke kusa da PREMIER HOTEL.
“Na shaida masa cewa to ni dai Bola Tinubu ne ya aiko ni cewa ya na son ganin ka, ido-da-ido kai da shi.
“Sunday ya ce min ai kuwa ina jin labarin Tinubu, ana ce min ai mutumin kirki ne. Saboda haka ni ma zan so ganin sa.
“Sunday ya ce amma ba zai so zuwa ganin Tinubu ba, saboda shi dan PDP ne, Tinubu kuwa dan ACN ne.
“A karshe dai ya amince zai gana da Tinubu, a bisa sharadin kada sanatan da ya dauke shi sojan-haya ko Pa Adedibu ya san an yi ganawar. Ni kuma na yi masa alkawarin haka.
Yadda Bola Tinubu Ya Rika Yi Wa Sunday Igboho Magiya Saboda Zabe:
“Nan da nan na sanar da Tinubu cewa Sunday Igboho ya amince su hadu. Shi kuma Tinubu ya garzayo daga Lagos, ya tare a SUNVIEW HOTEL a Akure, babban birnin jihar Ondo.
“Daidai karfe 10 na dare Sunday Igboho ya shigo otal din, ni da Tinubu mu ka gana da shi.
“Tinubu ya ce masa, Sunday, na ji labarin an dauke ka sojan-hayar tarwatsa rumfunan zabe. To ni rokon da na ke maka, kai da yaran ka ku bari a yi zabe, idan PDP ta yi nasara, shikenan. Idan kuma ANC ce ta yi nasara, shikenan.
“A karshe dai ya amince cewa babu dabanci, babu jagaliyanci a rumfunan zabe. Kuma ba za su saci akwatunan kuri’u ba. Ya ce ba ma za su shiga rikicin ba.
“Duk wannan abu da ake ciki, shi Fayemi dan takarar ACN bai ma sani ba. Kuma kun ji yadda aka yi har muka samu ACN ta yi nasara a zaben.
“Tinubu ya san a bi shi cikin katafaren dakin da ya sauka. Bayan mun fito na mika masa sakon sa, sai Sunday Igboho ya ce wa Tinubu, “Baba na gode da wannan babbar kyauta haka. Mu kuma na yi maka alkawarin babu wani takadarin da zai tayar da hankali a wurin zabe.
“Kun ji irin godiyar da ya yi wa Tinubu, saboda irin makudan kudaden da ya dumbuza masa.
Mugu Shi Ya San Makwantar Mugu:
“Sunday Igboho ya ce min to shi da yaran sa za su je Ekiti ranar jajibirin zabe. Amma ya na so karfe 2 daidai na dare, na kira shi, idan ya dauka zai kunna wayar yadda sauran yaran sa ‘yan-takifen zabe za su ji maganar da mu ke yi.
Sunday ya ce min da na kira shi ya dauka, to na ce masa ni ne AIG na ‘Yan Sanda, wato Mataimakin Sufeto Janar. Wai na ji labarin ya shigo Ekiti. Saboda haka ga ya nan zuwa nan da minti 30.
“Ya ce to a lokacin zai ce wa yaran sa kawai mu bar garin domin jami’an tsaro na niyyar yi masu kofar-raggo.
“Daga lokacin ya zama kusa da mu, har ya na ba mu labarai na rayuwar sa da siyasar sa.
Ya ce shi ma babban gogarman Lamidi Adedibu wajen dabancin siyasa da jagaliyanci a Ibadan.
Yadda Tinubu Ya Biya Kudin Otal Din Da ‘Yan-takifen Zaben Ekiti Su Ka Sauka:
Tun sati daya kafin zabe Tinubu ya kame dakunan da su Sunday Igboho za su zauna a Ekiti. Ya yi haka ne domin idan za su bar garin bayan na yi masu waya, to za mu tabbatar ba a bar ko dan-takife daya a cikin garin ba.
“Hatta jami’an INEC da jami’an tsaro a lokacin zaben rasa dakuna su ka yi wasun su. Sai da su ka bi ta hannu nan a roki Tinubu aka samar masu wasu dakuna. Ta haka mu ka san inda kowa ya ke zaune.
“Ranar Juma’a daidai karfe2 na dare, na kira Sunday na yi masa barazanar cewa ni AIG ne. Nan da nan ya hada kan’yan-takifen sa su 50 su ka bar garin cikin dare. Amma bayan sun bar garin sai ya kira ni, ya ce sun nemi mutum biyu ba su gani ba.
“Ashe mutum biyu din sun je gidan karuwai ne, ba su nan aka shirya ficewa. Sunday ya roke ni, ya ce idan an gano su, na sa su fito daga garin.
“Wajen karfe 5 ba asubahi, aka gano su. Na dauke su na kai su gida na. Wajen 6 na yamma na sa direba ya kai su wajen gari. Su ka shiga mota su ka fice.
“To kun dai ji yadda aka yi na san Sunday Igboho, gogarman da a yanzu ya yi suna inda ya bai wa Fulanin Ibarapa da ke Oyo wa’adin ficewa daga yankin.
“Ina kira a samo bakin zaren, a bar manoma su rika noma ba tare da ana garkuwa, kisa ko yi wa mata fyade ba.
“Gwamnati ta tashi tsaye a wanzar da zaman lafiya, wadda aka ce ta ta fi zama dan sarki.”
Babafemi Ujudu shi ne Mashawarci Na Musamman Ga Shugaba Muhammadu Buhari A Fannin Siyasa.