RASHIN TSARO: Buhari ya kori Buratai, da sauran manyan hafsoshin sojojin Najeriya, ya nada sabbi

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sallami manyan hafsoshin sojojin Najeriya tare da babban hafsan tsaron Kasa Gabriel Olomoshakin, ya nada sabbi nan take.

A sanarwar wanda Femi Adesina ya wallafa a shafinsa ta twita Buhari ya umarci babban hafsan sojojin Najeriya, Tukur Buratai, na Dakarun sama Sadique Abubakar da na ruwa kowa ya kama gaban sa daga yau litinin sannan ya musanya su nan take.

Wadanda aka nada sun hada da Leo Irabor babban hafsan tsaro, I Attahiru, Babban Hafsan Sojojin Najeriya, AZ Gambo, Sojojin ruwan Najeriya da IO Ilao, Babban Hafsan sojojin saman Najeriya.

Share.

game da Author