Sabuwar kididdigar da aka fitar a Najeriya ta bayyana cewa akalla rayukan mutum 348 ne su ka sawanta, sannan kuma aka yi garkuwa da mutum 411 cikin watan Disamba din da ya gabata a Najeriya.
Kashe-kashen da garkuwar duk akasari sun fi alaka ne da ta’addanci da kuma hare-haren ‘yan bindiga.
Haka dai wani rahoto da aka sa wa suna Najeriya Cikin Disamba, 2020 ya tabbatar.
Wata kungiya ce mai suna Nigeria Mourns, ta fitar da adadin kididdigar.
Rahoton shi ne lissafin kashe-kashe da hare-haren garkuwa da kungiyar ta fitar na karshen shekarar 2020.
Dukkan adadin kuma an tsakuro ne daga iyakar rahotannin da jaridu ke bugawa kadai.
Wannan ya nuna kenan duk wani kisa ko garkuwar da ba a bada labari a cikin jarudu ba, to ba su cikin lissafi kenan.
Rahoton ya nuna a cikin Disamba, 2020 an kashe farar hula 315, sauran 33 kuma duk jami’an tsaro ne.
An kuma kama mutum har 411 an yi garkuwa da su a cikin Disamba, kamar yadda bayanan da aka tattaro a cikin jaridu su ka tabbatar.
Jihar Barno ce aka fi kashe mutum har 70, sai kuma sauran jihohi su ka biyo baya kamar haka:
An dai yin kididdigar ce a jihohi 27 da su ka hada da:
Borno – 70, Kaduna – 64, Niger – 26, Katsina – 24, Ogun – 23, Zamfara – 19, Benue – 17, Edo – 17, Delta – 14, Ebonyi – 13, Adamawa – 8, Oyo – 6, Ondo – 6, Bayelsa – 5, FCT – 5, Lagos – 5, Rivers – 4, Plateau – 3, Imo – 3, Cross River – 3, Kogi – 3, Jigawa – 3, Taraba – 2, Anambra – 2, Kano – 1, Osun – 1 sai kuma Jihar Enugu – 1.
‘Yan bindiga sun kashe mutum 136, Boko Haram sun kashe mutum 66, sai kuma wasu 60 da aka kashe a rikice-rikicen kungiyoyin asiri.
Akwai kuma saran da aka kashe a rikice-rikicen manoma da makiyaya da kuma rikicin kabilu.
Discussion about this post