RAMUWAR GAYYA: Mahara sun kashe mutum 14, sun ji wa wasu da dama rauni a Kaya, jihar Kaduna

0

Bayan fatattakar wasu gungun ‘yan ta’adda da ‘yan bangan garin Kaya dake karamar hukumar Giwa, Jihar Kaduna, suka yi ranar Juma’a a wasu kauyuka da ke kusa da su, a ranar Asabar, maharan sun dira garin don daukan fansa.

Maharan sun dira garin Kaya da misalin kaefe 6:30 na yammacin ranar Asabar.

” Sun zo akan babura suna harbi ta ko-ina. Sun kashe mutum 14 sannaan sun ji wa wasu da dama rauni”. Inji wani mazaunin garin kaya.

Haka kuma mahara sun kina shagunan mutane, syn kona motoci da babura.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna ya tabbatar da aukuwa wannan mummunar lamari, in da ya ce maharan sun afjawa mutanen garin Kaya ne domin daukar fansan kashr wasu daga cikin abokan aikin su da ‘yan banga suka yi.

Aruwan ya bada sunayen wadanda aka kashe kamar haka, Hudu Shafiu, Madaro Madaki, Ibrahim Hamida, Ibrahim Mohammed Maidoya, Kabiru Maitakalmi, Ibrahim Kayawa, Danladi Daiyabu, Zubairu Mailemu, Awwalu Yahaya, Audu Sarkar da Maharazu Adamu.

Wadanda aka ji wa rauni kuma wanda yanzu haka suna asibin koyar na jami’ar Ahmadu Brllo dake Shika sun hada da Mujahideen Muhammad, Suleiman Mustapha Bashir, Ibrahim Sulaiman, Nuhu Idris, Alkassim Ismail , Nafi’u Sirajo, Musa Magaji, Muhammad Salisu Kaya da Musa Ibrahim.

Sai dai yace tuni jami’an tsaro sun fantsama domin ragargaza wadannan yan ta’adda da suka aikata wannan mummunan abu.

Share.

game da Author