RAHOTON MUSAMMAN: Yadda Hadiza Bala da Abubakar Malami su ka raba Atiku da kamfanin INTELS

0

Yanzu dai ta bayyana cewa Atiku ya kwashe dukkan makudan kudaden hannayen jarin sa daga kamfanin INTELS, wanda shi da wani Baturen kasar Italy su ka kafa.

Babban aikin INTELS dai tsawon shekaru ya hada da karbar wa Gwamnatin Tarayya kudaden haraji a tashoshin jiragen ruwan Najeriya. Shi kuma idan ya tara kudaden, zai damka wa gwamnatin na ta kaso, ya cire kamashon sa.

Hawan mulkin Buhari sai aka bijiro da wasu ka’idoji cewa INTELS ya rika tara dukkan kudaden da ya tara a Asusun Bai Daya Na Gwamnatin Tarayya (TSA) da ke Babban Bankin Najeriya (CBN).

INTELS ya ki amincewa da wannan ka’ida bisa dalilin cewa wasu kudaden da ya ke gudanar da ayyuka a tashoshin jiragen ruwa, duk a bankunan da ya ke tara kudin ya ke rantowa. Sai kudin haraji sun taru sannan bankin zai cire na sa.

INTELS ya nuna idan kudi su ka shiga asusun TSA to ba a san ranar da za a rika biyan sa kamashon sa ba. Wannan ne musabbabin tankiya tsakanin Atiku, INTELS da Gwamnatin Buhari.

Daga ranar 21 Ga Mayu, 2017 zuwa 8 Ga Disamba 2017, PREMIUM TIMES Hausa ta rika bibiyar wannan kwatagwangwama, inda ta buga labarin rikicin daban-daban sau tara (9).

TSAKANIN INTELS, ATIKU DA GWAMNATIN BUHARI: Wane Ne, Makaryaci, Mai Gaskiya Ko Munafiki?

Ranar 4 Ga Satumba, 2020, Gwamnatin Najeriya ta soke jarjejeniyar kwangilar da ke tsakanin ta da INTELS. Aranar 4 Ga Janairu, 2021 Atiku Abubakar ya bayyana kammala kwashe hannayen jarin sa kakaf a INTELS, ya na mai cewa Gwamnatin Buhari ce ta takura shi domin neman durkusar da shi.

Duk da har yau gwamantin Buhari ba ta maida martani ba, kamfanin INTELS ya maida raddin cewa babu wata matsalar da ta shiga tsakanin sa da gwamnatin tarayya, sai wata ‘yar rashin fahimta kawai.

PREMIUM TIMES HAUSA ta tattaro masu asali da tushen rikicin, domin mai karatu ya yi alkalanci, shin tsakanin Atiku, INTELS da Gwamnatin Tarayya, wane ne mai gaskiya? Wane ne makaryaci? Sannan wane ne munafiki?

Tushen Rikici:

RANAR 21 GA MAYU, 2017: Kiki-kaka A Kan Raba Riba Da TSA: Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta sa kafar wando daya da INTELS, babban kamfanin da Atiku ke takama da shi.

A ranar 15 Ga Maris, Manajar Daraktar NPA, Hadiza Bala Usman, ta rubuta wa kamfanin INTELS wasika cewa ta na so kamfanin ya rika aiki da sharuddan raba ribar aikin tara kudin haraji ta hanyar zuba kudaden a Asusu Daya Tilo na Babban Bankin Tarayya, CBN, maimakon a rika zuba kudaden a bankunan ‘yan kasuwa.

A cikin wasikar ne Hadiza ta tsara sabon sharadin raba riba tsakanin NPA da INTELS. Ta ce kamfanin INTELS zai rika daukar kashi 28 bisa 100 na ribar a matsayin ladar kamasho.

Sauran kashi 72 na ribar za a sake raba shi gwamnati na da kashi 30: yayin da INTELS zai dauki kashi 70.

Shi dai tsarin Asusun Bai Daya na TSA, an shigo da shi ne domin a rika tara duk wasu kudaden shiga da gwamnati ke samu a cikin asusu daya, yadda za a hana wawura da karkatar da kudade.

Sai dai a gefe daya kuma ana kuka da tsarin domin hakan na hana yawaitar shigar kudade a cikin asusun da ke karkashin bankinan ‘yan kasuwa.

Amma a ranar 27 Ga Maris, INTELS ya maida amsar wasikar shugabar NPA, sai dai duk da ya amince da sabon tsarin raba ribar, sai dai kuma ya ce ba zai iya amince zuba kudade a asusun TSA ba.

“Ke ma kin san bankunan da INTELS ke mu’amala da su, ba za su yarda mu rika zuba kudi a Asusun TSA da ke CBN ba.” Haka Babban Shugaban INTELS Andrew Dawes ya rubuta wa Hadiza, inda ya kara cewa, “ai idan mu na yin haka, za mu kasance babu ko sisi a hannun mu da za mu rika gudanar da ayyuka. Hakan kuma mun tabbatar NPA ba za ta so ya faru ba.”

A tsarin NPA, dukkan ribar da aka samu sai an fara zuba ta dungurugum a asusun TSA da ke CBN tukunna.

Sai dai kuma a wata wasika da NPA ta aika wa INTELS a ranar 19 Ga Afrilu, ta ce tilas ko dai kamfanin ya bi ka’idojin da ta shar’anta, ko kuma a soke kwangilar dungurugum. Inda ta kara cewa ta yi wa INTELS kawaici da jinkai inda ta yarda su rika yin ajiya a wasu bankuna biyu kacal baya ga TSA a CBN.

RANAR 28 GA YUNI, 2017: GOBARA DAGA TEKU: Yadda Kamfanin Atiku Ya Maka Gwamnatin Najeriya Kotu :

INTELS ya zargi gwamnati da karya yarjejeniya, inda hakan ya ce wata kullalliya ce domin yi wa kamfanin sa zagon-kasa. Tuni da Premium Times Hausa ta samu kwafen takardun bayanan shari’ar da za a tabka a kotu.

A cikin watan Mayu, hukumar tashoshin jiragen ruwa ta shaida wa kamfanonin da ke hada-hada a tashoshin sakon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, cewa an karkasa ayyukan tashoshin zuwa matakai uku: Na manyan jirage, jirage masu safarar kwantinoni da kuma jirage masu karakaina.

Sannan kuma an sake tsari a tashar jiragen ruwa ta Onne wadda kamfanin INTELS mallakar Atiku ne ke kula da hada-hada a tashar.

A takaice kenan gwamnati za ta bude tashar a matsayin mai karbar kowane irin jirgin safara, maimakon jiragen Lodi da jigilar fetur da gas kadai.

Wannan tasha ta Onne ita ce tasha mafi muhimmanci wajen jada-hadar fetur da gas a Najeriya, kuma a cikin ta ake cutar da kashi 65 bisa 100 na abin da ake fitarwa kasashen waje, a cewar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasa.

Amincewar da Shugaban Kasa ya yi, ta na kuma dauke da cewa “kowane mai shigo da kaya a cikin kasar nan, ya na da ‘yancin zabar tashar da zai rika sauke kayan da ya kawo daga waje.”

A takaice dai wannan bayani na nufin an karya lagos kaka-gidan da kamfanin INTELS na Atiku ya yi kenan.

Nan da nan sai Intel’s ya garzaya Babbar Kotun Tatayya ta Abuja, inda ya kalubalanci wannan tsari. A cikin sammacen kotu, INTELS ya na karar hukumar tashoshin jiragen ruwa, ministan shari’a, da kuma uwa-uba gwamnatin tarayya wacce dama ita ce a farkon wacce aka maka a kotun.

Takardar karar wadda aka gabatar wa kotun tun a ranar 4 Ga Yuni, ta nina cewa sabon tsarin da da aka shigo da shi ya karya yarjejeniyar da gwamnati ta kulla da INTELS a ranar 25 Ga Oktoba, 2005.

A wannan rana ce dai aka amince wa INTELS kula da hada-hada a tashoshin Warri biyu, wato tsohuwa da sabuwar tasha, tashar Kalaba da kuma ta Onne A da Onne B.

Takardar yarjejeniyar ta Nina cewa an kulla amincewar yin harkokin ne har tsawon shekaru 25.

RANAR 13 GA YULI, 2017: Martanin Hadiza Bala: Dalilin da ya sa muka dakatar da kamfanin Atiku (INTELS):

Shugabar Hukumar Tashoshin Ruwan Najeriya (NPA) Hadiza Bala Usman ta fadi wasu dalilan da ya sa hukumar ta dakatar da kamfanin INTELS’ wanda mallakin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ne Atiku Abubakar daga ci gaba da more iko da ta ke da shi na aiki ita kadai a tashoshin ruwar kasar.

Ta ce an yi haka ne domin ba wasu kamfanoni damar gudanar da irin ayyukan da kamfanin INTELS’ din ke yi a tashoshin ruwan.

Hadiza ta fadi haka ne a wata hira da ta yi da gidan Jaridar Daily Trust.

Ta ce hukumar tashoshin ruwan ba ta yi haka ba don ta muzguna wa kamfanin INTELS’ cewa ta yi haka ne domin kowa ya samu damar shiga harkar dako da adana mai da iskar gas a tashoshin kasar maimakon barin kamfanin INTELS’ din ya na cin karen sa ba babbaka.

Da aka tambaye ta game da zargi da ake yi cewa hukumar ta yi haka ne don dakile hanyoyin samun kudin sa saboda hana shi takarar shugaban kasa a 2019, Hadiza ta ce wannan maganar kanzon kurege ne amma ba haka suke nufi ba da dakatar da kamfanin INTELS’.

Ta ce har zuwa lokacin da aka dakatar da kamfanin INTELS kamfanin bai bude asusun nan na bai daya da kowace ma’aikata ta koma wato TSA ba. “ Idan aka tuntube kamfanin kan haka sai ya ce zai yi amma shiru. Sannan kuma shugaban kasa da kan sa ya umurce mu da a sakar wa kowa ikon iya gudanar da aiki a tashoshin ruwar kasar.”

RANAR 12 GA OKTOBA, 2017: WASA YA BACI: Atiku da Gwamnatin Buhari sun raba hanya:

Kamfanin INTELS mallakar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya mayar wa gwamnatin tarayya kakkausan martani, dangane da soke yarjejeniyar kwangilar shekaru 17 da gwamnatin baya ta ba kamfanin.

A yarjejeniyar da aka yi da Intel tun shekarar 2010, an rattaba hannu cewa INTELS ne zai rika karbar kudaden haraji daga manyar jirajen ruwa masu kwasa da sauke lodi a tashoshin kasar nan.

Sai dai kuma bayan hawan gwamnatin APC, gwamnatin da Atiku ya taka muhimmiyar rawar kafuwar ta da samun nasarar ta, sai aka fara tunaninn yadda za a soke wannan kwangila da INTELS ke yi.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya rubuta wa Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, Hadiza Bala cewa ta soke kwangilar ta dala miliyan 70 duk shekara, a bisa hujjar cewa ta saba wa doka ta sashe na 8(1) da kuma na 162(1).

An dai bai wa INTELS wannan kwangila ce tun cikin 2010, wanda a ranar 27 Ga Satumba, 2017, Malami ya ce a soke ta bayan an kwashe shekaru bakwai ana gudanar da ita.

Kamfanin INTELS ya maida zazzafan martani a jiya Laraba, ya na mai shaida wa gwamnatin Najeriya cewa soke kwangilar dungurugum da aka yi ranar Talata, 10 Ga Oktoba, 2017, “sakarci ne, shashanci ne, wauta ce kuma abin dariya ne.”

INTELS ya kara da cewa soke wannan kwangila zai yi wa Najeriya mummunar illa.

RANAR 21 GA OKTOBA, 2017: PREMMIUM TIMES HAUSA ta bi diddigin rikicin, a wani rahoton da ta saw a suna. “Bayan Tiya, Akwai Wata Caca.”

RANAR 16 GA NUWAMBA: SIYASA ROMON JABA: An kori ma’aikatan Atiku daga Najeriya:

Jiya Laraba ne Gwamnatin Tarayya ta soke takardar iznin zama Najeriya da aka bai wa wasu kwararrun ma’aikatan kamfanin INTEL’S Nigeria Limited, da wasu kamfanoni biyar. INTELS dai mallakar tsohon mataimakin shugaban kasa ne, kuma jigo a jam’iyyar APC, wato Atiku Abubakar.

Hukumar Shige-da-fice ta Nijeriya, ta bayyana sunayen sauran kamfanonin da korar ta shafa, sun hada da PREDECO International Limited, West AFRICA Monetary Services Limited, Net Global System, MGM Logistics Solutions Limited ada kuma ORIEN Investment.

Ma’aikatan da korar da ritsa da su a cikin kamfanonin shida, an ba su makonni biyu, zuwa nan da 30 Ga Nuwamba da su tattare komatsan su su fice daga Najeriya. Idan ba haka ba kuwa, to za a yi musu mokar-kare a bisa umarnin Ministan Harkokin Cikin Gida.

Babban Kwantirola na Shige-da-fice, Muhammad Babandede, shi ne ya bayyana wannan soke takardar iznin zama da aka yi musu a Abija ta bakin kakakin yada labaran hukumar, Sunday James.

Ya na mai karawa da cewa dokar kasar nan ta sashe na 39, karamin sashe na 1 daga cikin dokar shige-da-fice ta 2015 a shashe na 5 karamin sashe na 5 ne ya bada ikon yin korar.

RANAR 27 GA NUWAMBA: INTELS ya amince zai bi dukkan ka’idojin da Gwamnatin Tarayya ta shimfida masa. Wannan amincewa da INTELS ya yi domin bin sharuddan gwamnati, ya sa bangarorin biyu sun sasanta, kamar yadda PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin sanantawar a RANAR 8 GA DISAMBA, 2017.

RANAR 5 GA SATUMBA, 20120: An soke yarjejeniyar kwangila tsakanin INTELS da Gwamnatin Tarayya dungurugum.

RANAR 4 GA JANAIRU, 2021: Atiku ya bayyana kammala kwashe dukkan makudan hannayen jarin sa daga INTELS, tare da zargin gwamnatin Buhari da kokarin karya shi.

RANAR 7 GA JANAIRU, 2021: Sauran masu rike da kamfanin INTELS sun maida raddin cewa babu wani rikicin da ya taba faruwa tsakanin INTELS da Gwamnatin Tarayya. An dai samu rashin fahimtar da nan ba da dadewa ba ana fatan warware ta.

Share.

game da Author