Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu, ya umarci dukkan Fulani makiyaya da ke zaune cikin dazukan jihar (forest reserves), su fice daga cikin dajin nan da kwanaki bakwai.
Umarnin ko kuma dokar ya fara aiki ne daga ranar Litinin 18 Ga Janairu, 2021.
Akeredolu ya bada wannan umarnin ne a lokacin da ya yi ganawa tare da shugabannin Fulani makiyaya da kuma shugabannin kabilar Ebira da ke jihar.
Taron ya gudana a Babban Dakin Taro na Cocoa Conference Hall da ke cikin Gidan Gwamnatin Jihar Ondo a Akure, babban birnin jihar.
Akeredolu ya ce an dade ana fama da hare-hare da garkuwa da mutane waɗanda wasu bɓatagari ke yi da fakewa da kiwo amma su na garkuwa da mutane a jihar.
“A yau mun ɗauki babban matakin farko na daƙile garkuwa da mutane da saukar manyan laifukan da ake aikatawa a faɗin jihar nan.”
“Yawancin waɗannan ayyukan garkuwa da mutane wasu ɓatagari ne ke yin su masu fakewa da sunan makiyaya. Sun maida dazukan gwamnati wata maɓuyar masu garkuwa da mutane, su na karɓar makudan kuɗaɗen diyya.
“A matsayi na na Gwamnan Jiha wanda nauyin kare hakkin rayuka da dukiyoyin jama’a ke hannun sa, ina sanar da bijiro da wadannan ka’idojin da gaggawa, wadanda su ka hada da:
Tsauraran Dokoki 6 Da Gwamnatin Ondo Ta Kakaba Wa Makiyaya:
1. Makiyaya su gaggauta ficewa daga dukkan dazukan gwamnati da ke cikin jihar Ondo, nan da kwanaki bakwai, daga ranar Litinin 18 Ga Janairu, 2021 za su fara kirgawa.
2. An haramta kiwo cikin dare, saboda yawancin gonakin da makiyaya ke cinye wa amfanin gona, duk da dare ake yin aika-aikar.
3. An haramta zirga-zirgar shanun kiwo a kan manyan titina da kuma cikin gari.
4. An haramta kiwo ga duk wani yaron da ba balagi ba.
5. An umarci dukkan jami’an tsaron da ke Jihar Ondo su tirsasa bin wannan dokar tilas.
6. Amma gwamnatin mu mai tausayi ce, don haka duk wani mai son yin kiwo a jihar nan, to ya gaggauta yin rajista da hukumar da nauyin kula a kiwo ke kan ta.