Gwamnatin jihar Kano ta raba injinan banruwa 5,000 wa manoma domin inganta aiyukan noman rani a jihar.
Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Murtala Sule-Garo ya bayyana haka a zantawa da yayi da manema labarai ranar Laraba a garin Kano.
Sule-Garo ya kuma ce gwamnati ta tura ma’aikatan noma don taimakawa manoma sanin dabarun aikin gona na zamani a duk kananan hukumomi 44 dake jihar.
Bayan haka gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya ta raba wa manoma takin zamani, maganin feshi, irin da sauran kayan aikin gona.
Gwamnati ta kashe Naira biliyan 2 wajen horas da matasa da mata sana’o’in hannu a jihar.
PREMIUM TIMES HAUSA a watan Disemba ta buga labarin yadda Ministan Harkokin Noma Sabo Nanono, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta yi wa manoma milyan biyar rajistar samun tallafin takin zamani a cikin rahusa da rangwame.
Nanono ya ce za su samu rahusar tallafin ne daga Shirin Wadata Manoma da Taki na Ofishin Shugaban Kasa, wato PFI.
Cikin 2016 Gwamnatin Buhari ta kirkiro Shirin PFI domin kawadaitawa da tallafawa wajen samar da takin zamani a cikin kasa, da nufin a rage dogaro da shigo daga waje da ake yi.
Baya ga haka taki a cikin kasa, shirin PFI ya ta’allaka wajen ganin takin zamani ya karade yankunan kasar nan, ya wadaci manoma.