NNPC na fadada ayyukan ta fiye da dogaro da man fetur kadai –Kyari

0

Shugaban NNPC Mele Kyari, ya bayyana cewa hukumar NNPC ta dukufa ka’in da na’in wajen fadadawa da bunkasa sabbin hannoyin rage dogaro da man fetur kacokan a Najeriya.

Ya ce a yanzu hana NNPC na ci gaba da fadada ayyuka da kadarorin hukumar fiye da dogaro da komai daga danyen man fetur.

Hakan inji Kyari, ya faru ne saboda tasirin da makamashi ya samar a duniya.

Mele Kyari, wanda shi ne Babban Manajan Daraktan NNPC, ya yi wannan jawabi ne a cikin wata takarda da ya gabatar a “Taron Manyan Masana Dabarun Makamashi na Duniya na UAE na 2021.

Takardar Kyari ta bada fifiko ne kan tasirin wannan dabara a Afrika da Najeriya a zamanin da babu korona nan gaba.

“Mu yanzu a Najeriya, NNPC ta maida hankali sosai wajen fadada harkokin ta fiye da dogaro kacokaan kan feur. Ana ci gaba da karkata zuwa amfani da gas a gidaje masu dimbin yawa yanzu haka a Najeriya.

“Sannan kuma NNPC na tallafawa wajen gudanar da bincike, kirkiro sabbin dabaru da bijiro da fasahohi, bunkasa dabarun amfani da sola da sauran hanyoyin buunkasa makamashi da dama.

Ya ce NNPC za ta ci gaba da gudanar da wadannan tsare-tsaren bunkasawa da fadada amfani da makamashi a yanayin da ake ciki na fama da annobar korona.

“Za mu ci gaba da kara zuba jarin mu a fannin makamashi ta hanyar rika fitar da gas a kasuwannin dunniya da inganta amfani da shi a cikin gida.

“Sannan abin farin ciki a wannan harkar shi ne, kasuwa ce ke bukatar makamashin, ba wai neman yadda za a yi da shi ake yi ba. A koda yaushe jama’a da kasuwa na cikin bukata.

A karshe ya yi kiran kasashen Afrika su bi sabon tafarkin tsiran tattalin arzikin da Najeriya ta bi.

Share.

game da Author