NECO ta dage ranar fara jarabawar kammala Sakandare na kowa da kowa (External)

0

Hukumar shirya Jarabawar Kammala Sakandare na kowa da kowa wato (External) na shekarar 2020 ta canja ranar da za a fara jarabawar.

Kafin canja ranakun fara jarabawar, za a fara jarabawar ne ranar 1 ga Faburairu sannan a gama ranar 3 ga watan Maris.

Kakakin hukumar Azeez Sanni, ya bayyana cewa maimakon ranakun 1 ga Faburairu zuwa 3 ga Maris, yanzu za a fara jarabawar ne daga 8 ga Faburairu zuwa 10 ga Maris.

Azeez ya kara da cewa hukumar ta dauki wannan mataki ne domin a ba dalibai dama su kammala yin rajistar jarabawar.

Bayan haka NECO ta umarci daliban da basu samu damar yin wasu daga cikin jarabawar karshe na NECO saboda hargitsin #EndSARS, su yi amfani da wannan dama su garzaya wuraren rubuta jarabawar su rubuta darussana da ba su yi ba.

Share.

game da Author