Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Najeriya za ta karbi maganin rigakafin cutar korona na Pfizer da BioNTech 100,000 a karshen watan Janairu.
Shugaban hukumar cibiyar kiwon lafiya na matakin farko na ƙasa, NPHCDA Faisal Shuaib ya sanar da haka ranar Talata a ganawa da kwamitin PTF ta yi da manema labarai a Abuja.
Shuaib ya ce kamfanin COVAX wanda ya dauki nauyin shigo da magungunan zai shigo da kwalaben maganin 100,000 sannan daga baya kamfanin ya kara shigowa da miliyan 42 na maganin a matsayin gudunmawar kamfanonin vaccine alliance da GAVI wa Najeriya.
Ya ce maganin rigakafin guda miliyan 42 din da za a shigo da su zai kunshi ire-iren magungunan rigakafin cutar da hukumomin kula da lafiya na duniya suka amince da su sannan daga ciki zai isa ayi wa akalla kashi 20 bisa 100 na mutum miliyan 200 da ke kasar nan.
Idan ba a manta ba gwamnati ta kafa kwamitin mutum 18 wanda za su tabbatar Najeriya ta samu maganin rigakafin cutar korona da zaran hukumomin lafiya sun amince da shi.
Duk da wannan kokari da gwamnati ta yi wasu kwararrun ma’aikatan lafiya sun bayyana ra’ayoyin su wa PREMIUMTIMES cewa da wuya Najeriya ta fara yi wa mutane allurar rigakafi a watan Janairu ganin yadda kasashen duniya da dama ke layin samun a basu maganin don mutanen su.
Kwararrun sun kuma ce a yanzu haka Najeriya bata da wurin ajiyan wadannan magunguna koda an shigo da su kasan.
Shu’aib ya ce bayan an kammala lissafi za a sanar wa mutane adadin yawan kudaden da za a bukata wajen shigo da raba maganin a kasar nan.
Zuwa yanzu mutum 91,351 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 75,699 sun warke, 1,318 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 14,267 ke dauke da cutar a Najeriya.