Cibiyar Binciken Lakanin Hada Magunguna ta Kasa, NIPRD, ta bayyana cewa ta gano wasu sinadarai da lakanin da idan an harhada za a iya samar da maganin warkar da cutar Korona.
Sai dai kuma Babban Daraktan Cibiyar Pharmaceutical Research and Development (NIPRD), Obi Adigwe ne ya bayyana haka yayin da ya kira wani taron manema labarai a ranar Litinin, wanda PREMIUM TIMES ta da cikakken bayanin da daraktan ya gabarar.
Adigwe ya bayyana cewa sun gano lakani sadidan wanda wato ‘Nipprimmune’, wanda gidigat ne kuma sadidan zai yi maganin cutar korona.
Sai dai kuma ya yi korafin cewa rashin tallafin kudaden aikin bincike da hada maganin zuwa ruwan allura ko kwayoyi ne cikas din da su ka hadu da shi.
“Tun kimanin tsawon shekara daya kenan, mu ka yi amfani da kwarewa da kuma fasahar kimiyyar da muka koya, har muka gano cewa Nipprimmune’ zai iya maganin cutar korona.” Inji Adigwe.
“A wancan lokacin fa mun rika karade gidajen talbijin daban-daban, mu na sanar da abin da muka binciko, tare da rokon masu tallafawa su shigo ciki a yi hadin guiwar sa kudade domin mu karasa abin da ya rage kafin mu kai gacin tabbatar da maganin, har ya wadata yadda za a rika amfani da shi.”
Najeriya ta kafa wannan cibiya da zimmar yin amfani da sinadarai da lakanin kayan gida, ana kirkiro magunguna.
Sai dai Adigwe ya ce rashin zuba wa cibiyar kudin ayyukan da za ta aiwatar da binciken ta ta yi ne ke kawo wa cibiyar cikas.
” Babu wata kasar da ta ci gaba da ba ta kashe akalla kashi 1 zuwa 5 na karfin tattalin arzikin cikin gidan ta wajen inganta harkokin bincike.”
“Wadancan kasashe da su ka san abin da su ke yi, su na kashe nunki 100 na abin da mu ke kashewa wajen gudanar da bincike.”
Daga nan sai ya ce Najeriya a matsayin ta na kasar da ta fi sauran kasashen Afrika yawan jama’a da karfin arziki, bai kamata a ce ita ce a sahun baya wajen kulawa da bincike ba.
Ya ce akalla cibiyar sa ta rubuta wasika ga cibiyoyi da hukumomi da kamfanoni sun kai 30, domin a hada karfi a samar da maganin cutar korona a Najeriya, amma kamar an shuka dusa.
Discussion about this post